‘Dan Jarida Yana Karar Hon. Doguwa a Kotu, ‘Dan Majalisa Ya Yi Masa Mahangulba

‘Dan Jarida Yana Karar Hon. Doguwa a Kotu, ‘Dan Majalisa Ya Yi Masa Mahangulba

  • Abdullahi Yakubu ‘dan jarida ne wanda yake karar Hon. Alhassan Ado Doguwa a gaban wani kotun majistare
  • Lauyoyin da suka tsayawa Abdullahi Yakubu sun ce ‘Dan majalisar ya doke shi ne har kunnensa ya fara ciwo
  • A yunkurin lallashin ‘Dan siyasar a wajen taron ‘yan jarida, wannan ya yi sanadiyyar da ya sha naushi a kunne

Kano - Wani ‘dan jarida ya shigar da karar Alhassan Ado Doguwa mai wakiltar Tudun-Wada/Doguwa a majalisar wakilan tarayya na kasa.

‘Dan jaridar yana tuhumar ‘dan majalisar na jihar Kano da laifin gwabje shi. Jaridar Daily Nigerian ta kawo wannan labari a ranar Larabar nan.

Abdullahi Yakubu mai aiki da gidan jaridar Leadership yace Hon. Alhassan Ado Doguwa ya auka masa ne wajen taron manema labarai a Kano.

Kara karanta wannan

Mai Neman Takara Ya Shigar da Karar Jam’iyyar NNPP Saboda An Yi Waje da Sunansa

A korafin da ya rubutawa wani kotun majistare da ke garin Kano, ‘dan jaridar yace Doguwa ya doke masa kunnen dama sa’ilin da yake lallashinsa.

Abdullahi Yakubu ya tanadi Lauyoyi

Lauyoyin ‘dan jaridar, Bashir Ahmad, Umar Umar da Hamisu Abdulwahab sun fadawa kotu wannan ya faru ne a taron ‘yan jarida a ranar Talata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mu na masu kare Malam Abdullahi Yakubu na rukunin gidajen Sharada a birnin Kano, mu na masu rubuta maka wannan takardar korafi.
Wanda muke ba kariya kwararren ‘dan jarida ne mai aiki da jaridar Leadership, kuma shi ne shugaban gidan jaridar na shiyyar nan ta Kano."

- Bashir Ahmad, Umar Umar da Hamisu Abdulwahab

Alhassan Ado Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa a Majalisa Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

Doguwa ya kira taron 'yan jarida

A bayanan da lauyoyin suka bada, sun ce ‘dan majalisar ya gayyaci ‘yan jarida domin ya yi masu bayanin abin da ya faru tsakaninsa da Murtala Sule Garo.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Yi Tsami, Alhassan Doguwa ya Fasa-bakin Kakakin APC a Gaban Jama'a

"Ganin yadda ya fusata, sai wanda muke ba kariya ya tunkare shi, ya lallashe shi (Alhassan Doguwa) da ya yi hakuri, ka da ya dauki doka a hannu.
A maimakon shi ya saurari wanda muke ba kariyan, ya yi abin da ya kamata, sai ya dauki hannunsa na dama, ya yi masa gwabza a kunnen dama.
Tun daga lokacin wanda muke ba kariya yake fama da rashin lafiya, ya samu matsala a dodon kunnensa da ciwon kai, gabobin jiki da sauransu."

- Bashir Ahmad, Umar Umar da Hamisu Abdulwahab

Lauyoyin su na nema alfarma, a umarci AIG na rundunar ‘yan sanda ke shiyyar Kano ya binciki lamarin, domin a hukunta Hon. Alhassan Ado Doguwa.

Ado Doguwa ya bugi Kakakin APC

A rahoton da aka samu jiya, an ji labari bayan abin da ya faru tsakanin Alhassan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo, an sake yin wata arangamar a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: APC Ka Iya Shan Kaye a Zaben 2023, Doguwa Ya Magantu Bayan Barkewar Sabon Rikici

Hon. Alhassan Ado Doguwa ya naushi Ahmad Aruwa a lokacin da ya zo gidansa yayin da ake taro, Kakakin na APC ya bar wajen bakinsa yana jini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng