Abin da ya Haddasa Fadanmu da Murtala Garo a gidan Gawuna - Alhassan Doguwa

Abin da ya Haddasa Fadanmu da Murtala Garo a gidan Gawuna - Alhassan Doguwa

  • Hon. Alhassan Ado Doguwa ya yi bayanin yadda rigima ta kaure tsakaninsa da Murtala Sule Garo
  • ‘Dan majalisar yace Murtala Garo ya fara zagin shi, ya nemi ya yi fada da shi daga zuwa inda ake taro
  • Doguwa ya musanya zargin cewa shi ya ji wa tsohon Kwamishinan rauni, yace ba haka abin yake ba

Kano - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya yi bayanin abin da ya haddasa sabani tsakaninsa da Murtala Sule Garo.

Daily Nigerian ta fitar da rahoto na musamman a kan rigimar da ta kaure tsakanin Alhassan Ado Doguwa da Murtala Sule Garo a wajen taron jam'iyya.

Wata majiya ta shaidawa jaridar da Hon. Alhassan Doguwa ya isa gidan Nasiru Gawuna inda ake zaman APC, ya koka kan yadda aka ware shi a gefe.

Kara karanta wannan

Mutuwar Ifeanyi: Kwankwaso, Hadimin Buhari Da Sanata Orji Kalu Sun Mika Ta’aziyyarsu Ga Davido Da Chioma

‘Dan majalisar wakilan kasar ya fadawa jagororin APC ba a neman shi a kan abubuwan da suka shafi kudi, sai dai idan za ayi wa jam’iyya wani aiki.

Wannan ya jawo rikici ya shiga tsakaninsa da Murtala Garo mai takarar mataimakin gwamna. 'Dan siyasar yace ba shi ya yi wa abokin fadansa rauni ba.

Ba fada ya kai ni ba - Doguwa

Da ya zanta da manema labarai a ranar Talata, Hon. Doguwa yace bai je wajen taron jam’iyyar domin fada da Garo ba, ya je ganin shugaban jam’iyya ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alhassan Ado Doguwa
Hon. Alhassan Ado Doguwa Hoto: @alhassan.doguwa
Asali: Facebook
“Ban je da nufin halatar taron ba, na je ganin Abdullahi Abbas ne, in yi tafiya ta.
Da na isa gidan Gawuna, na shiga dakin taron, sai na iske ana zama. Sai nayi ba’a ga mataimakin gwamna, nace ya kamata a samu wakilci daga majalisa.

Kara karanta wannan

Ganduje Ba Zai Ruguza Mani Gida ba, ko da a kan Layin Lantarki aka Gina Inji Rarara

- Alhassan Ado Doguwa

Murtala ya fara zage-zage

Sai Murtala ya tsoma baki, ‘dole ne a gayyace ka?’, dole ne a gayyaci ‘yan majalisar tarayya.
Sai ya fara dirka mani zagi “banza maras mutunci, dan uban ka ba za a gayyace ka ba”.

- Alhassan Ado Doguwa

Ban ji masa ciwo ba - Doguwa

“Ban maida masa martani ba saboda ina da tarbiyya. Sai ya cigaba da zagi na, har ya nemi ya ja mani riga, daga nan nayi fushi, na fara martani.
Ta kai ya nemi ya ci kwala ta, a yunkurin zuwa ya yi fada da ni, akwai kofi a kan tebur, Sai Murtala Sule Garo ya bugi kofin da ya fadi, ya tarwatse.

- Alhassan Ado Doguwa

Manufofin Kwankwaso

An samu rahoto Rabiu Kwankwaso mai takara a inuwar NNPP ya yi alkawari zai ba talaka damar zuwa makarantun gaba da sakandare idan ya ci zabe.

Kamar yadda ya yi yunkuri a Majalisar Dattawa, Gwamnatin Kwankwaso za ta sa sakamakon JAMB ya yi shekaru hudu kafin ya daina aiki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel