Mai Neman Takara Ya Shigar da Karar Jam’iyyar NNPP Saboda An Yi Waje da Sunansa

Mai Neman Takara Ya Shigar da Karar Jam’iyyar NNPP Saboda An Yi Waje da Sunansa

  • Auwal Isiyaku Seiko ya dauki hayar Lauya, ya maka jam’iyyarsa ta NNPP a babbar kotun jihar Gombe
  • ‘Dan siyasar yana kalubalantar hana shi takarar ‘Dan Majalisar dokokin Jihar Gombe a zabe mai zuwa
  • Seiko yace shi ne ya lashe zaben fitar da gwani a Jam’iyyar NNPP, amma sai aka bada tikiti ga wani dabam

Gombe - Auwal Isiyaku Seiko mai neman zama ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Gombe a majalisar dokokin jiha, zai yi shari’a da jam’iyyarsa.

Kamar yadda Aminiya ta fitar a wani rahoto a ranar Laraba, 2 ga watan Nuwamba 2022, an ji Auwal Isiyaku Seiko yana karar jam’iyyarsa ta NNPP.

Auwal Isiyaku Seiko ya shigar da kara ta hannun lauyansa a babban kotun jihar Gombe, saboda an cire sunansa a matsayin ‘dan takara a 2023.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso Ya Yi Alkawarin Maida WAEC, NECO, JAMB Kyauta Idan Ya Gaji Buhari

Sauran wadanda Auwal Seiko ya maka a kotu sun hada da hukumar zabe na kasa watau INEC da abokin takararsa, Adamu Muhammad Sabon Riga.

‘Dan siyasar yana ikirarin shi ne wanda ya lashe zaben fitar da gwani da NNPP ta shirya kwanaki, amma aka tsaida Adamu Muhammad Sabon Riga.

Rahoton yace Auwal Seiko ya samu kuri’u 13 a cikin kuri’u 14 da aka kada a zaben tsaida ‘dan takaran majalisar dokoki na jiha a watan Yulin 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Khamisu Mailantarki a Gombe Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Yayin da hukumar INEC ta fitar da sunayen masu takarar ‘yan majalisar dokoki a zaben 2023, sai Seiko ya fahimci an maye gurbinsa da na Sabon Riga.

HN Nwoye ya tsayawa Auwal Isiyaku Seiko

HN Nwoye shi ne wanda ya shigar da kara a babban kotun mai zama a Gombe a madadin Auwal Seiko, kuma an soma shari’a tun a watan Oktoban jiya.

Kara karanta wannan

Ka yi kadan: Gwamna Wike Ya Aikawa Shugaban Jam’iyyar PDP Sabon Raddi

Kotu ta aika sammaci ga wadanda ake tuhuma da laifi a wannan shari’a, amma ba su samu zuwa gaban Alkali ko su aiko lauyoyin da za su tsaya masu ba.

Da yake bayani, Lauyan mai kara watau HN Nwoye yace jam’iyyar NNPP, hukumar INEC da abokin karawar wanda ake karewa sun san da zaman kotun.

Magatakardar kotun yace bai san dalilin kin zuwansu ba domin sun sanar da wadanda ake kara. HIO Ufoma ya daga karar sai 4 ga watan Nuwamba.

Shari'a a Ekiti

Kun ji labari tsohon Kwamishinan shari’an Ekiti yace shi ya tsayawa Ayo Fayose a shari'o’in da aka yi da shi lokacin da ‘Yan Majalisa suka tsige shi daga mulki.

Owoseni Ajayi wanda Lauya ne yace kamfaninsa ya ba tsohon gwamnan kariya da EFCC ta taso shi a gaba, amma ba a biya shi kudin aiki ba, yana neman N950m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel