Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

Tsohon Na Hannun Daman Kwankwaso Ya ki Yarda Ya yi Aiki a Kwamitin Kamfen Peter Obi

  • Aminu Dabo ya fitar da jawabi bayan ganin sunan shi a cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben Peter Obi
  • Tsohon kwamishinan na jihar Kano yace har gobe yana nan a APC, babu abin da ya hada shi da Jam’iyyar LP
  • Dabo wanda ya rabu da Kwankwasiyya ya shiga APC a gabanin zaben 2019 ya yi kira ga Obi ya fasa takara

Kano - Aminu Dabo ya maida martani na musamman a sakamakon ganin sunansa da ya yi a cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben Peter Obi a 2023.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talata, inda aka ji Hadimin ‘dan siyasar, Abdullahi Usman ya fitar da jawabin nesanta kan shi daga jam’iyyar LP.

Abdullahi Usman yace tsohon ‘dan takaran gwamnan na jihar Kano cikakken ‘dan jam’iyyar APC ne wanda babu abin da ya hada shi da yakin zaben Obi.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

Arch. Aminu Dabo ya tabbatar da cewa ba zai karbi wannan aiki ba, yana mai karawa da cewa ba a tuntube shi domin jin ta bakinsa kafin fitar da sunansa ba.

Ba za a zauna a Jam'iyyu 2 a lokaci daya ba

‘Dan siyasar yace a matsayinsa na ‘dan jam’iyyar APC mai rajista kuma jigo a jihar Kano da matakin tarayya, ba za ta yiwu ya yi wa wata jam’iyya aiki ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Ina bada hakurin cewa dole in yi watsi da wannan mukami. Har yanzu ni ‘dan jam’iyyar APC ne.
Peter Obi
Peter Obi a taron ICAN Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Zan dage wajen ganin nasarar Asiwaju Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima da kuma ‘yan takaran APC na zaben Gwamna, Dr Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo a zaben 2023 mai zuwa."

- Aminu Dabo

Kara karanta wannan

Ziyarar da Peter Obi Ya Kai wa Dr. Ahmad Gumi ta Jawo Masa Bakin jinin Magoya baya

Jaridar tace Dabo yace yana goyon bayan takarar tsohon gwamnan Legas watau Asiwaju Bola Tinubu.

A matsayin daya daga cikin dattawa kuma jagororin APC a Kano, ina so in tabbatarwa Duniya da hidimata wajen ganin nasarar Asiwaju Tinubu/Kashim Shettima.

- Aminu Dabo

Dabo ya ba Peter Obi shawara

Dabo ya yabawa ‘dan takaran na LP saboda yadda ya nuna jajircewa wajen takarar kujerar shugaban kasa, yace ina ma zai hakura da neman mulki a 2023.

A jawabin, Dabo ya yi kira ga abokin na sa ya bi sahun Tinubu a APC, sannan ya yi godiya da har aka ga cancantar sa sunan shi a kwamitin yakin zaben LP.

Muna tare da Tinubu - El-Rufai

A jiya aka ji labari Nasir El-Rufai yace idan Ahmadu Bello da Tafawa Balewa suna Duniya, za su goyi bayan mutumin Kudu ya karbi shugabancin Najeriya.

Gwamnan na Kaduna kuma jigo a jam’iyyar APC ya yi wa Bola Tinubu alkawari cewa zai samu kuri’un mutanen yankin Arewacin Najeriya a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Na Tambayi Peter Obi a Zaman da Nayi da Shi inji Sheikh Ahmad Gumi

Asali: Legit.ng

Online view pixel