‘A Sa Ido’: Tinubu Ya Ware Masu Kula da Zaben Fitar da Gwanin Kujerun Majalisar Tarayya

‘A Sa Ido’: Tinubu Ya Ware Masu Kula da Zaben Fitar da Gwanin Kujerun Majalisar Tarayya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ware manyan masu mukamai a gwamnatinsa domin kula da zaben fitar da gwani a cikin APC
  • Tinubu ya zabi Femi Gbajabiamila da Ibrahim Masari alhakin sa ido kan zaɓukan fitar da gwani na APC na yar majalisar tarayya
  • Sabon tsarin zai haɗa Gbajabiamila da Masari da gwamnoni, shugabannin APC da majalisar tarayya domin tabbatar da sahihin zaɓen

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahotanni sun ce wasu manyan ’yan siyasa na matsa wa Bola Tinubu lamba ya faɗaɗa kwamitin kula da zaben fitar da gwani, amma shugaban ya ƙi.

Majiyoyi sun ce Shugaba Bola Tinubu ya ki amincewa da hakan domin kare tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyya wurin zabukan fitar da gwanin.

Tinubu ya bukaci sanya ido a zaben fitar da gwanin yan majalisa
Shugaba Bola Tinubu yayin da ganawa da shugabannin Majalisar dattawa. Hoto: @aonanuga1956.
Source: Twitter

Umarnin Tinubu kan zaben fitar da gwanin APC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, da mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, su jagoranci sa ido kan zaɓukan fitar gwani na APC, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yunwa a Arewa: Tinubu ya ware tireloli 100 na abinci, makudan kudi ga jihohi 19

Matakin na zuwa ne bayan tattaunawa tsakanin shugaban ƙasa da sanatoci da ’yan majalisar wakilai da suka buƙaci a tabbatar da dimokuraɗiyya cikin jam’iyyar APC.

Sabon tsarin zai bai wa Gbajabiamila da Masari damar aiki tare da gwamnoni, kwamitin gudanarwa na APC da shugabannin majalisar tarayya wajen gudanar da aikin.

Ana sa ran za su yi aiki tare da shugabannin jam’iyya domin tabbatar da cewa zaɓukan fitar da gwani sun kasance cikin lumana da gaskiya a faɗin ƙasa.

Tinubu zai saka ido kan zaben fitar da gwani na majalisar tarayya
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da mataimakinsa, Barau Jibrin. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Bangaren da kwamitin zai karkata a kai

Sai dai an bayyana cewa sabon tsarin ba zai maye gurbin aikin sakatariyar APC ta ƙasa ba wajen shirya da gudanar da zaɓukan fitar da gwani.

Kwamitin zai fi mayar da hankali kan haɗin kan siyasa, lura da bin doka da kuma taimakawa wajen warware rikice-rikicen da ka iya tasowa yayin da wasu sanatoci suka bukaci tikiti kai tsaye.

Sakatariyar APC ta ƙasa ce za ta ci gaba da fitar da sanarwa, tantance ’yan takara, tura kwamitocin zaɓe da kuma tattara sakamakon zaɓuka.

Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan ’yan siyasa na son a ƙara wasu mutane cikin tsarin sa idon domin biyan bukatun ɓangarori daban-daban, kamar yadda TheCable ta ce.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya bijirewa gwamna, ya yi fatali da zabin wanda zai gaje shi a 2027

Sai dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙi amincewa da hakan saboda gudun kada a raunana tsarin gudanar da sahihin zaɓen fitar da gwani a APC.

Tinubu ya yi fatali da 'bukatar' sanatoci

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya gana da Shugabannin majalisar dattawa a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya na Abuja.

Wasu sanatocin sun nemi a ba su tikitin takara mai tsaye wanda aka ce shugaban bai amince ba kuma ya nace cewa dole a mutunta tsarin jam’iyya.

Ganawar sirri da aka yi a Aso Villa ta mayar da hankali kan batutuwan kasa masu muhimmanci, inda aka ce an dauki matakai masu karfi ba tare da bayyana su ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.