Labaran garkuwa da mutane
Rundunrar 'yan sandan jihar Neja ta bayyana kame wasu mutum da ake zargin sun hallaka wani hakimi tare da sace 'yarsa da karbar kudin fansa a jihar da ke Arewa.
Tsagerun yan bindiga sun sace mata da dan hakimin kauyen Nasarawa a karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano inda suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Kwamishinan yan sandan Kano, CP Mamman Dauda, ya tabbatar da sace mataɗdagacin garin Nasarawa a karamar hukumar Tsanyawa da ke jihar ranar 2 ga watan Afrilu.
Miyagun yan bindiga da Kotu ta ayyanasu a matsayin 'yan ta'adda sun sace ɗaliban makarantat sakandiren jeka ka dawo a yankin karamar hukumar Kachia, Kaduna.
Wasu tsagerin yan bindiga kai hari, sun halaka mutane bakwai sannan suka yi garkuwa da wasu 26 a garuruwa bakwai da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja.
Wasu tsagerun 'yan bindiga sun sace daliban jami'a guda biyu a jihar Zamfara, inda suka kutsagidan kwanan dalibai don aikata wannan mummunan barna da suka yi.
Yayin da musulmai ke ta azumi, 'yan ta'adda sun ci gaba da aikata laifi a jihohin Arewacin Najeriya. Sun kashe mutane da yawa a jihar Katsina da ke Arewaci..
Kwanakin baya aka dauke wani Mai ba Gwamnan Zamfara shawara a kan siyasa. A makon nan Ibrahim Ma’aji ya kubuta daga hannun ‘yan bindiga bayan an biya kudi
Jami'an rundunar yan sanda a jihar Kogi sun yi nasarar ceto mutum 13 da aka yi garkuwa da su daga wani Otel da ke yankin Eleite a hanyar titin Lokoja-Ajaokuta.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari