Hukumar 'Yan Sanda Ta Bayyana Sunayen Bayin Allah da Aka Sace a Wurin Ibada a Katsina

Hukumar 'Yan Sanda Ta Bayyana Sunayen Bayin Allah da Aka Sace a Wurin Ibada a Katsina

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ta sanar da bayanan wasu da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a Kankara
  • A ranar Lahadi da safe, wasu miyagun 'yan bindiga suka kai hari Kauyen Mai Tsauni dake karamar hukumar Kankara
  • Dakarun 'yan sanda karkashin DPO sun yi hanzarin kai dauki amma suka taras yan ta'addan sun gudu

Katsina - Hukumar yan sanda reshen jihar Katsina ta fitar da bayanan mata biyar waɗan da 'yan ta'adda suka yi awon gaba da su a jihar Katsina da safiyar Lahadi.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa matan sun shiga hannun 'yan ta'addan ne a kauyen Mai Tsauni, Gidan Haruna a karamar hukumar Kankara yayin da suke hanyar zuwa Coci.

Yan sanda.
Hukumar 'Yan Sanda Ta Bayyana Sunayen Bayin Allah da Aka Sace a Wurin Ibada a Katsina Hoto: premiumtimes
Asali: UGC

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa, ya fitar yace 'yan bindigan dauke da bindigun AK-47 sun bude wa mutane wuta yayin harin.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya Sun Sheke Shugaban 'Yan Bindiga, Kachalla Gudau, Har Lahira a Katsina

Mista Isa ya bayyaɓa cewa yan ta'adda sun raunata Malamin Cocin New Life For All, wanda aka gano sunansa Haruna a takaice.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ƙara da cewa a halin yanzun Faston na kwance a Asibitin cikin garin Kankara ana masa magani.

Sunayen matan da maharan suka sace

A sanarwan Gambo isa ya bayyana sunayen matan da yan ta'adda suka yi garkuwa da su tare da shekarun su, inda ya ce:

"Wadan da aka sace su ne, Rabi Isyaku, mai shekara 15, Rabi Saidu, mai shekaru 36, Rabi Babba, 49, Saratu Hadi, 27, da kuma Nusaiba Shuaibu, yar shekara 13, duk daga kauyen Mai Tsauni, Kankara, jihar Katsina.”

Wane mataki jami'an tsaro suka dauka lokacin harin?

Isah ya bayyana cewa DPO 'yan sanda na Kankara ya samu labarin harin kuma nan take ya jagoranci Dakaru zuwa wurin amma suka taras yan ta'addan sun gama sun gudu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Miyagu Sun Kai Farmaki Coci a Katsina, Sun Yi Garkuwa da Mutum 25

Punch ta ruwaito Gambo Isah na cewa:

"DPO na Kankara ya jagoranci jami'an yan sanda zuwa kauyen amma tun kafin isarsu, yan ta'addan sun tsere da mutanen. Nan take suka dauki Faston zuwa Babban Asibitin Kankara."

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Matar Ma'aikacin Kamfanin NNPP a Osogbo

Rahotanni sun bayyana cewa an yi garkuwa da matar ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Jumu'a a gidanta dake yankin babban birnin jihar Osun.

Kwamandan jami'an Amotekun, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin yace ba zasu runtsa ba har sun kubutar da matar sun kamo maharan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel