Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malamin Addini a Jihar Ekiti

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malamin Addini a Jihar Ekiti

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun yI garkuwa da Malamin Coci yayin da yake hanyar koma wa gida a jihar Ekiti ranar Asabar
  • Bayanaai sun ce Rabaran Michael ya shiga hannun maharan ne a tsakanin kauyen Itaji da Ijelu Ekiti bayan ya baro Ado Ekiti
  • Har yanzu rundunar 'yan sanda ba ta ce komai ba kan harin amma wani Basarake ya ce jami'an tsaro sun ba zama da nufin ceto Malamin

Ekiti - Wasu tsagerun 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun yi awon gaba da fitaccen Malamin addinin Kirista a jihar Ekiti dake kudu maso yammacin Najeriya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun yi garkuwa da Malamin Majami'ar Katolika da ke Omu Ekiti, karamar hukumar Oye, Rabaran Fada Michael Olofinlade.

Harin garkuwa da mutane Ekiti.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malamin Addini a Jihar Ekiti Hoto: vanguardngr
Asali: UGC

An tattaro cewa Rabaran Olofinlade ya shiga hannun 'yan ta'addan ne a tsakanin kauyukan Itaji da kuma Ijelu Ekiti yayin da yake hanyar dawowa daga Ado Ekiti, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Yi Garkuwa da Matar Wani Ma'aikacin Kamfanin Mai Na Kasa NNPC

Basaraken gargajiya Owajumu na Omu Ekiti, Oba Adeyeye Ogundeyi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Basaraken ya kara da cewa tuni hukumomin tsaron kasar nan da haɗin guiwar Mafarauta suka baza komarsu ta ko ina da nufin ceto Rabaran din cikin koshin lafiya.

Har zuwa yanzu da muka hada maku wannan rahoton, hukumar 'yan sanda a jihar Ekiti ba ta ce uffan ba kan harin da kuma matakain da suke ɗauka na ceto shi.

Najeriya na fama da makamanta irin wadan nan hare-haren na garkuwa da mutane da kashe-kashe da mafi yawan shiyyoyin kasar nan musamman arewa.

An Yi Garkuwa da Matar Wani Ma'aikacin Kamfanin Mai Na Kasa NNPC

A wani labarin kuma wasu mutane da ba'a san ko su waye ba sun je har gidan sun tasa matar wani ma'aikacin kamfanin man fetur na kasa NNPC.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Halaka Basarake a Jihar Arewa, Gwamna Ya Kakaba Dokar Zaman Gida

Wasu miyagu sun yi awon gaba da matar wani ma'aikacin kamfanin man fetur na kasa NNPC a Osogbo, babban birnin Osun ranar Jumu'a da ta gabata.

Kwamandan Amotekun, Amitolu Shittu, ya baza Dakarunsa ta ko ina, ya tabbatar da cewa zasu dawo da matar kuma su damke makwamusan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel