"Ku Yaki 'Yan Bindiga"; Tsare Tsohon Malami Ya Jawo Abin Magana ga Gwamnatin Katsina

"Ku Yaki 'Yan Bindiga"; Tsare Tsohon Malami Ya Jawo Abin Magana ga Gwamnatin Katsina

  • Ƙungiyar CNG reshen Katsina ta yi Allah wadai da kamawa da tsare Dr. Bashir Kurfi, tana neman a sake shi ba tare da wani sharadi ba
  • Ta ce ya kamata gwamnatin Katsina ta fi mayar da hankali kan yaƙi da ƴan bindiga maimakon takura masu sukar gwamnati
  • CNG ta ce sukar manufofin gwamnati da neman a yi abin da ya dace hakki ne da kundin tsarin mulki ya tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Ƙungiyar Coalition of Northern Groups (CNG) reshen jihar Katsina ta yi Allah wadai da kama da ci gaba da tsare masanin harkokin jama'a, Dr. Bashir Kurfi.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen yaƙi da matsalar ƴan bindiga maimakon takura masu bayyana ra'ayoyinsu.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Yadda za a kai korafi ga EFCC kan zargin damfara, badakala

An soki gwamnatin Katsina kan tsare Dr. Kurfi
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai kula da ƙungiyar a jihar, Abdullahi Kabir, ya fitar.

Kungiyar CNG ta bayyana kama Dr. Kurfi a matsayin tsangwama ta siyasa, tare da neman a sake shi cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba.

Ta ce abin da ake zargin Dr. Kurfi da shi, shi ne bayyana damuwarsa kan tabarbarewar tsaro da kuma yadda gwamnati ke tafiyar da yaƙi da ƴan bindiga a jihar Katsina.

CNG ta ce an take haƙƙin faɗin albarkacin baki

A cewar CNG, amfani da rundunar ƴan sanda da kuma kotuna domin gurfanar da ɗan ƙasa saboda bayyana ra'ayinsa barazana ce ga dimokuraɗiyya, 'yancin faɗin albarkacin baki da kuma haƙƙoƙin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar wa ƴan ƙasa.

Ƙungiyar ta ce yayin da al'ummomi da dama a faɗin jihar Katsina ke ci gaba da fuskantar munanan hare-haren ƴan bindiga, rasa matsuguni da kuma rayuwa cikin fargaba, abin da hukumomi suka fi mayar da hankali a kai shi ne kulle bakin masu bayyana gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga: Kungiyar duniya ta yi wuf ta yi magana da jin an cafke malami a Katsina

Sanarwar ta ce:

"Ya kamata gwamnati ta fi mayar da hankali wajen yaƙi da masu ta'addancin da ke addabar al'ummominmu, ba wai tsananta wa ƴan ƙasa da ke magana a madadin waɗanda abin ya shafa ba."

CNG ta nuna damuwa kan tsarin shari'ar

Ƙungiyar ta kuma yi zargin cewa ana ƙoƙarin ci gaba da tsare Dr. Kurfi ta hanyar tuhume-tuhume da ta bayyana a matsayin marasa tushe da kuma amfani da tsarin shari'a ta hanyar da ba ta dace ba.

Har ila yau, CNG ta ce wannan lamari ya ƙara jawo damuwa kan shirin kafa rundunar ƴan sandan jihohi, tana mai gargadin cewa idan ba a kare hukumomin tsaro daga katsalandan na siyasa ba, za a iya amfani da su wajen gallaza wa ƴan adawa, 'yan jarida, masu fafutuka da sauran masu bayyana ra'ayoyi mabambanta.

An taso gwamnatin Katsina a gaba
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

CNG ta yi kira ga gwamnati da ƴan sanda

Ƙungiyar ta jaddada cewa sukar manufofin gwamnati da neman a yi abin da ya dace bai kamata a ɗauke su a matsayin laifi ba, tana mai cewa yin magana kan batutuwan da suka shafi jama'a haƙƙi ne da kundin tsarin mulki ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban ma'aikatar bogi ya yaudari mataimakin shugaban majalisar wakilai

Saboda haka, CNG ta bukaci a saki Dr. Bashir Kurfi nan take ba tare da wani sharadi ba, sannan a kawo ƙarshen tsoratar da 'yan jarida, masu sharhi, masu fafutuka da sauran ƴan ƙasa masu bayyana ra'ayoyinsu kan shugabanci da tsaro.

Hakazalika, ta yi kira ga rundunar 'yan sandan Najeriya da kada ta bari a yi amfani da ita wajen farautar abokan adawar siyasa, maimakon haka ta mayar da hankali wajen yaƙi da ƴan bindiga da sauran manyan laifuka a jihar Katsina da sauran jihohin da matsalar tsaro ta shafa.

Kotu ta umarci a tsare Dr. Kurfi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Wata Kotun Majistare da ke jihar Katsina ta bayar da umarnin tsare Dr. Bashir Kurfi, a hannun 'yan sanda.

Alƙalin kotun, Mai Shari'a Zaharaddeen Kofar Soro, ne ya bada umarnin bayan rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta gurfanar da Dr. Kurfi bisa zargin bata suna da kuma yaɗa labaran ƙarya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com