Edo: An Kama Sarakunan Gargajuya Biyu da Hannu a Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa

Edo: An Kama Sarakunan Gargajuya Biyu da Hannu a Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa

  • An damke Sarakunan gargajiya guda biyu bisa zargin alaka da harin garkuwa da fasinjojin jirgin kasa a jihar Edo
  • Kwamishinan sadarwa na Edo ne ya bayyana haka ranar Laraba amma bai ambaci sunayen sarakunan da aka kama ba
  • Tun farko gwamnatin jihar Edo ta gargaɗi cewa duk Basaraken da ta gano da hannu zai ɗanɗana kudarsa ba zata daga kafa ba

Edo - A ranar Laraba 18 ga watan Janairu, 2023, gwamnatin jihar Edo ta bayyana cewa an damƙe Sarakunan gargajiya biyu da hannu a harin da yan ta'adda suka kai tashar jirgin kasa.

Jaridar Tribune ta ce gwamnatin ta sanar da cewa ana zargin Sarakunan da alaƙa da harin wanda aka yi garkuwa da Fasinjoji akalla 20 masu jiran jirgin kasa daga tashar Igueben zuwa Warri, jihar Delta.

Kara karanta wannan

Katsina: An Yi Nasarar Kubutar da Daya Daga Cikin Mutanen da Yan Bindiga Suka Sace a Wajen Bauta

Jirgin kasa.
Edo: An Kama Sarakunan Gargajuya Biyu da Hannu a Garkuwa da Fasinjojin Jirgin Kasa Hoto: tribuneonline
Asali: UGC

Kwamishinan sadarwa da wayar da kai na jihar Edo, Mista Chris Osa Nehikhare, wanda ya sanar cafke sarakunan bai ambaci sunayensu ba.

Daily Trust ta rahoto kwamishinan na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Labari mai daɗi game da garkuwan shi ne an kama mutane 7 da Sarakunan gargajiya biyu masu alaƙa da faruwar lamarin."

Ya kara da cewa jami'am tsaro sun ceto ragowar mutum biyu dake hannun yan ta'addan.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton yadda wasu yan bindiga suka kai hari tashar jirgin sanar Asabar 7 ga watan Janairu, 2023 suka yi awon gaba da Fasinjoji.

Idan baku manta ba, daga komawarsa Benin City ranar Lahadi, Gwamna Godwin Obaseki, ya zargi gwamnatin tarayya da rashin samar da ingantaccen tsaro a tashar jirgin.

Obaseki ya ce duk da abinda ya faru da jirgin kasa mai jigila daga Kaduna zuwa Abuja, FG ba ta dandara ba kuma ya zargi Sarakunan gargajiyar yakin da rashin kula da iyakarsu.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Dan sandan da bindige lauya mai juna biyu ya musanta zargin kisa

Tun kafin faruwar haka, gwamnatin Edo ta gargaɗi cewa babu Basaraken da zata ɗaga wa kafa matukar bincike ya gano cewa yana da hannu a aikata muggan laifuka a yankunan da ke karƙashinsa.

'Yan Sanda Sun Kama Makamai a Zamfara, Sun Gano Mutum Biyu Da Ake Zargi

A wani labarin kuma Jami'an rundunar yan sanda sun ci karo da wasu mutum biyu mace da namiji dauke da makamai a jihar Zamfara

Jami'in hulɗa da jama'an na rundunar 'yan sandan jihar, Muhammad Shehu, yace an kama mutanen da Alburusai sama da 300 da bindigar Ak-47.

Yace sun amsa laifinsu an safarar makamai daban-daban ga 'yan bindihan jeji a jihar da wasu jihohi masu makwaftaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel