Abin Tausayi: Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Yi Magana kan Rasuwar 'Ya'yansa 2

Abin Tausayi: Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Yi Magana kan Rasuwar 'Ya'yansa 2

  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya ce ya rungumi mutuwar ‘ya’yansa biyu a matsayin ƙaddara daga Allah SWT
  • Mustapha Baba Tela da Ummi Baba Tela sun rasu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Bauchi zuwa Azare
  • Har yanzu mutum uku na ci gaba da jinya sakamakon hatsarin da ya faru a kusa da kamfanin shinkafa na Tiamin Rice

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela, ya ce ya ɗauki mutuwar ɗansa, Mustapha Baba Tela, da ‘yarsa, Ummi Baba Tela, a matsayin ƙaddara daga Allah.

‘Ya’yansa sun rasu ne a ranar Asabar, 4 ga Yulin 2026, bayan motar da ke ɗauke da su ta yi mummunan hatsari a titin Bauchi zuwa Azare, kusa da kamfanin Tiamin Rice, kimanin kilomita 20 daga birnin Bauchi.

Kara karanta wannan

Kurunƙus: Tinubu ya mika fam ga APC, ya zabi wanda zai masa mataimaki a zaben 2027

Sanata Baba Tela.
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Sanata Baba Tela Hoto: Abdulkadir Adamu
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa yaran suna hanyar dawowa Bauchi ne bayan halartar bikin auren ‘yar uwarsu a Azare, lamarin da ya sauya farin cikin iyali zuwa babban alhini.

Sanata Baba Tela ya dauki kaddara

Da yake magana cikin jimami da hawaye, Sanata Baba Tela ya ce babu wanda zai iya ƙalubalantar hukuncin Allah SWT.

Ya ce:

“Na ɗauki mutuwar ‘ya’yana biyu a matsayin ƙaddara daga Allah. Mun san cewa abin da Allah Ya ƙaddara ne zai faru, ba za mu iya tambayar nufinsa ba. Idan Ya ga dama, zai iya ɗaukar rayukanmu gaba ɗaya lokaci guda.”
“Allah Ya tsara komai tun kafin halittar duniya. Shi Ya ba mu su, kuma Shi Ya karɓe su. Babu wanda zai iya ƙalubalantar hukuncinsa.”

Wasu ‘ya’yan Baba Tela na asibiti

Sanatan ya bayyana cewa wasu daga cikin ‘ya’yansa da suka ji rauni a hatsarin suna ci gaba da karɓar magani a asibiti.

Ya ce har yanzu bai samu ƙarfin zuciyar yin ƙarin bayani ba, yana addu’ar Allah Ya ba su lafiya cikin gaggawa, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bangar siyasa suka hallaka wani fitaccen malamin Islamiyya a Bauchi

FRSC ta bayyana musabbabin hatsarin

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC), reshen Bauchi, ta ce hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Asabar a kusa da kamfanin Tiamin Rice.

Hukumar ta bayyana cewa motar Toyota Prado mai lambar KTG 253 SM ce ta yi hatsarin, kuma Auwalu Babatela ne ke tuƙa ta.

Hukumar FRSC ta danganta hatsarin da karya dokar fitilar hanya da kuma tuki cikin haɗari.

Bauchi.
Taswirar jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutane shida ne ke cikin motar, inda mutum huɗu suka samu raunuka, yayin da Mustapha Baba Tela da Ummi Baba Tela suka rasu a wurin da hatsarin ya faru.

Kwankwaso ya miƙa ta'aziyya ga Baba Tela

A wani labarin, kun ji cewa ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya mika ta'aziyyarsa ga tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Baba Tela.

Kwankwaso ya aika da sakon ta'aziyyar ne bisa rasuwar yayansa biyu, Mustapha da Ummi, a wani mummunan hatsarin mota.

Ya bayyana lamarin a matsayin wata babbar kaddara mai ban takaici da ta haifar da firgici da alhini mai yawa ba wai kawai ga gidan da aka yi rashin ba, har ma da Masarautar Katagum da ma daukacin jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262