'Yan Bindiga Sun Kutsa Yankin FCT, Sun Halaka Uba Tare da Sace 'Ya'Yansa 2

'Yan Bindiga Sun Kutsa Yankin FCT, Sun Halaka Uba Tare da Sace 'Ya'Yansa 2

  • Firgice da tashin hankali ya darsu a zukatan mazauna anguwar Ushafa na yankin Bwari da ke FCT, yayin da wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka shiga yankin a safiyar Laraba
  • An tattaro yadda lamarin ya faru misalin karfe 1:00 na dare, inda 'yan bindigan suka shiga yankin gami da daukar sama da minti 30 suna harbe-harben ba tare da jami'an tsaro sun dakatar dasu ba duk da akwai bariki kusa da yankin
  • Haka zalika, sun halaka wani mutumi gami da sace yaransa biyu yayin da yayi bata kashi dasu, inda suka bar matarsa kwance riris saboda tsananin ciwon da ta ke yi

FCT, Abuja - Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a safiyar Laraba sun shiga anguwan Ushafa a yankin Bwari na Babban Birnin Tarayya (FCT), inda suka halaka wani sannan su ka yi garkuwa da 'ya'yansa biyu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Zabgegiyar Damisa Tana Takun Isa Cikin Jama'a Da ke Shakatawa ya Janyo Cece-kuce

'Yan sanda
'Yan Bindiga Sun Kutsa Yankin FCT, Sun Halaka Uba Tare da Sace 'Ya'Yansa 2. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

An tattaro yadda lamarin ya faru misalin karfe 1:00 na dare, wanda hakan ya jefa firgici ga mazauna yankin da suka saba da zaman lafiya, jaridar Leadership ta rahoto.

Wata mazauniyar yankin, Mrs Veronica David, ta bayyana yadda lamarin ya faru bayan wata firamaren gwamnati a Ushafa, kusa da tashar Okada, Channels Tv ta rahoto.

Ta bayyana yadda 'yan bindigan, wadanda suka shiga yankin, suka budewa jama'an wuta fiye da minti 30 ba tare da jami'an tsaro sun dakatar dasu ba, duk da akwai wata bariki kusa da yankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Daga bayanin da muka samu, mutumin, Mr. Adegoke, wanda aka halaka yayi kokarin ja-in-ja da 'yan bindiga saboda yadda suka yi kokarin tafiya da dukkansu. Wannan shi ne dalilin da yasa suka bindige shi har lahira.
"Bayan sun halakasa, masu garkuwa da mutanen sun fara harbi ba kakkautawa gami da yin awon gaba da 'ya'yansa biyu zuwa wani gurin da ba a san ko ina bane, ta saman tsaunuka."

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

- A cewarta.

Haka zalika, wani mazaunin yankin, Abdul Abbas, ya ce lokacin da yaji karar harbin bindiga a lokacin da suke tsaka da harin, yayi tunanin 'yan bindiga ne suka shiga anguwar.

"A wannan gabar, abun da na iya yi shi ne addu'ar neman dauki daga Ubangiji.Tun da nake a wannan anguwar ban taba jin irin wannan harbin bindigar ba.
"Mun yi imani da cewa, 'yan bindigan sun yi niyyar shiga gidaje da dama a wannan anguwan, amma saboda bata-kashin da suka yi da mutumin da suka kashe, dole tasa suka bar anguwar da gaggawa. Muna bukatar karin tsaro a wannan wurin saboda muna cikin firgicin sake faruwar lamarin."

- Kamar yadda ya kara.

Wani sifetan 'yan sanda a anguwar Ushafa, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda a cewarsa ya janyo firgici ga mazauna yankin da dama gaba daya daren.

"Kafin 'yan sandan su kawo agaji, makasan sun tsere. Amma bayanin da muka samu shi ne, sun halaka wani mutumi da yayi bata-kashi da su gami da yin awon gaba da yaransa biyu. Sun so tafiya da matarsa, sai dai tana kwance riris kuma ba za ta iya tafiya ba, wannan ne dalilin da yasa suka bart a nan."

Kara karanta wannan

Kaduna: ‘Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Yankunan Birnin Gwari, Sun Halaka Jami’an Tsaro

- A cewarsa.

'Yan bindiga sun farmaki Birnin Gwari, sun halaka jama'a

A wani labari na daban, wasu miyagu sun kai mugun hari karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Sun halaka jami'an NSCDC har su bakwai tare da wasu mutanen gari duk a fushinsu bayan halaka wani yaro da ke musu kiwon shanu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel