Bincike Ya Tona Yadda Alkalin CCT Ya Karkatar da Miliyoyi zuwa Asusun Matarsa

Bincike Ya Tona Yadda Alkalin CCT Ya Karkatar da Miliyoyi zuwa Asusun Matarsa

  • Sunan matar Danladi Yakubu Umar ya fito a shari’ar da ake yi tsakanin alkalin na CCT da lauyoyin hukumar EFCC
  • Binciken jami’an yaki da cin hanci da rashawa ya tono yadda ‘yan kwangila suka rika aika wa matar alkalin kudi
  • Mai dakin shugaban kotun CCT, Zulaihatu Danladi Umar ta samu N15,587,833.76 ta hannun wasu kamfanoni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Bayanai da ba a san da su ba a baya, sun nuna yadda ake zargin Danladi Yakubu Umar ya karkatar da makudan kudi da yake ofis.

Ana zargin cewa N15.5m sun bar asusun wasu zuwa akawun din matar Danladi Yakubu Umar a lokacin yana shugabantar kotun nan ta CCT.

Danladi Umar
Tsohon shugaban kotun CCT, Danladi Umar Hoto: Danladi Umar
Source: Facebook

Danladi Umar ya samu miliyoyi daga kujerar CCT

A zargin da hukumar EFCC ta ke yi wa alkalin da ake tuhuma, Daily Nigerian ta ce akwai amfani da ofishinsa na CCT wajen azurta kan shi.

Kara karanta wannan

Yadda alkalin CCT ya casa Tinubu, Saraki da sauran manya kafin ya kare a kurkuku

Danladi Umar ya shugabanci majalisar da ke sa ido a rabon kwangiloli a kotun da’ar ma’aikatan da ke lura da dukiyoyin masu mukamai.

Ana zargin ya rika umartar ‘yan kwangilar da ke aiki a kotunsa su tura wa matarsa kudi ta banki.

Kamfanoni sun rika aika wa matar Danladi kudi

Tuhumar farko da ake yi wa wanda ake zargi a gaban U. P. Kekemeke shi ne ya wani da aka ba kwangila ya aika wa Zulaihatu Danladi Umar kudi.

Binciken lauyoyin EFCC ya faro tun daga Oktoban 2021 da aka ce kamfanin Kurchmives International Limited ya yi kwangilar yi wa hedikwatar fenti.

Kamfanin ya karbi kwangilar ne daga Momanaf Global Ventures Limited wanda shi aka fara ba aikin.

Wannan kamfani ne ya tura wa matar alkalin N5.5m a wani asusunta da ke bankin Keystone. Idan ta tabbata, an saba wa sashe 19 na dokar ICPC ta kasa.

Danladi Umar
Danladi Umar lokacin yana shugabancin kotun CCT a Abuja Hoto: Economic and Financial Crimes Commission (EFCC)
Source: Facebook

Zargi na biyu shi ne a Junairun 2024 wani takwaran wancan kamfani, Portal Realities Limited ya sake aika wa matar N6m a asusunta da ke bankin Zenith.

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta tura tsohon shugaban CCT ta Najeriya gidan yari a Abuja

Masu binciken sun ce kamfanin JTF Global Links Ltd ya samu kwangilar zamanantar da bayanan kotun don haka ya samu ladar ofis a dalilin hakan.

Sauran kudin da matar ta karba ta asusun bankinta ya kai adadin zuwa N15,587,833.76. Zargin da alkalin ya karyata a lokacin da aka karanto masa su.

Zargin shugaban CCT da neman cin hancin N10m

ICiR ta ce tun 2013 EFCC ta ke zargin alkalin ya nemi cin hancin 10m daga hannun wani jami’in kwastam, Rasheed Owolabi da ake shari’a da shi.

Owolabi ya fada wa hukuma ya biya N1.8m ta asusun wani hadimin alkalin. Da ake shari’a da Ali Gambo Abdullahi a kotu a 2017, zancen ya taso.

Danladi Umar: Wadanda suka sha matsar alkalin CCT

Ana da labari kotu ta tura tsohon shugaban CCT, Danladi Umar gidan yari. Kafin nan mun tattaro yadda ya kula da shari'o'in wasu manyan kasa.

An dauko manyan shari'o'in da shugaban kotun CCT da aka tsare a kurkuku a yau ya jagoranta a baya a lokacin da ludayinsa yake kan dawo.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tsohon shugaban alkalai, Walter Onnoghen da tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki sun yi shari'a gaba shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng