Jaruman ’Yan Banga Sun Kwamushe Wasu ’Yan Ta’adda 5 a Jihar Bauchi

Jaruman ’Yan Banga Sun Kwamushe Wasu ’Yan Ta’adda 5 a Jihar Bauchi

  • Wasu 'yan bindiga a jihar Bauchi sun gamu da tashin hankali yayin da 'yan banga suka tarfa su, suka kame su
  • Jami'in gwamnati ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma bayyana yabo ga 'yan bangan tare da kara musu kwarin gwiwa
  • Ana ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda a bangarori daban-daban na Najeriya, musannan a shekarar nan

Alkaleri, jihar Bauchi - Akalla ‘yan ta’adda biyar ne suka shiga hannun ‘yan banga a wani yankin karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

An ruwaito cewa, wadannan ‘yan ta’adda sun dade suna aikata ayyukan ta’addanci kan mazauna a jihar Bauchi kafin dubunsu ta cika, Tribune Online ta ruwaito.

An ce kamun nasu na zuwa a ci gaba da aikin kakkabe ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

An kama 'yan bindiga a Bauchi
Jaruman ’Yan Banga Sun Kwamushe Wasu ’Yan Ta’adda 5 a Jihar Bauchi | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Shugaban kwamitin riko na karamar hukumar, Hon. Baka Ibrahim Alkaleri ya sanar da kama masu garkuwa da mutanen, inda yace an kama su ne a kauyen Mansur da ke gundumar Gwana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar sanarwar da ya fitar, an kama ‘yan ta’addan ne a lokacin da jami’an tsaro ke sintiri kamar yadda aka umarce su da yi a yankin.

Bala Ibrahim ya yabawa ‘yan bangan da ma sauran jami’an tsaro bisa wannan manijin aikin kare kauyuka da garuruwa a jihar, National Accord ta tattaro.

Ya kuma bayyana cewa, za a ci gaba da ba jami’an tsaro da ‘yan sa kai kwarin gwiwa da goyon bayan fatattakar miyagu a yankinsa.

A bangare guda, shugaban y aba da umarni ga ‘yan banga da su yi sintirin kame ‘yan ta’adda, inda suka kama wasu tsageru biyu a yankin Pali tare da ceto mutum biyar da aka sace.

Kara karanta wannan

Ana bata sunan shugabanmu: Hukumar DSS ta fusata kan yadda ake cece-kuce game da Yusuf Bichi

Wasu ’Yan Bindiga Sun Kashe Wata Mata Mai Juna Biyu da Wasu Mutane Uku a Anambra

A wani labarin kuma, wasu 'yan bindiga sun hallaka wasu mutane hudu a jihar Anambra a Kudu maso Gabas.

A cewar majiya daga yankin, daya daga cikin mutanen da aka kashe wata mata ce mai dauke da juna biyu na watanni.

Ya zuwa yanzu dai an tattara gawarwakin mamatan, ana ci gaba da bincike kan lamarin mara dadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel