Ba Mu Taba Tunanin Dagewa Ko Soke Zaben 2023 Ba, Hukumar Zabe Ta INEC Ta Magantu

Ba Mu Taba Tunanin Dagewa Ko Soke Zaben 2023 Ba, Hukumar Zabe Ta INEC Ta Magantu

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa, bata taba tunanin dage zaben 2023 ba tun lokacin shirin yinsa na farko
  • Wannan na zuwa ne bayan da aka bayyana yiwuwar dage zaben ko soke shi a 2023 idan tsaro bai inganta ba
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da zaben 2023, kasancewar ana yawan samun hare-hare a bangarori daban-daban na kasar

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta magantu kan yiwuwar dage zaben 2023 da ke tafe nana da wata guda, BBC ta ruwaito.

Hukumar ta yi magana ne ta bakin shugabanta, Farfesa Mahmud Yakubu, inda yace hukumar bata taba tunanin dage zaben na 2023 ba.

Idan baku manta ba, INEC ta tsara yin zaben shugaban kasa ne a ranar 25 ga watan Fabrairu mau zuwa, kana zaben zai hada ne da na 'yan majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Zauna da Fastoci a Aso Villa, Ya Fada Masu Gaskiyar Batun Ɗaga Zabe

INEC ba za ta dage zabe ba, inji Mahmud Yakubu
Ba Mu Taba Tunanin Dagewa Ko Soke Zaben 2023 Ba, Hukumar Zabe Ta INEC Ta Magantu | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A bangare guda, za a yi zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha a cikin Maris mai zuwa ga mai rai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan tsaro bai inganta ba, za a dage zaben 2023

A bangare guda, a wani taro da aka gudanar a Abuja, hukumar ta yi magana, inda tace matukar harkar tsaro bata inganta ba a kasar, to za a dage zaben ko kuma ma soke shi gaba daya, rahoton Daily Trust.

Sai dai, a wannan karo INEC ta yi karin haske, inda tace sam babu shirin dage zaben tun farkon lokacin da take tsara jadawalin ayyukan zaben shekarar. A cewar shugaban na INEC a ranar Laraba 11 ga watan Janairu:

"INEC ba ta tunanin sauya jadawalin zaben ko kuma ma dage shi. Tabbacin da jami'an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma'aikatanmu ya karfafa mana gwiwar ci gaba da shirinmu cikin tsanaki."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatarwa Da Yan Nigeria Zai Ai Zabe A Watan Gobe Mai Kamawa

Ya bayyana kwarin gwiwar yin zaben na 2023 be a yayin wata ganawa da shugabannin jam'iyyun siyasa 18 a Abuja don sanar dasu halin da ake ciki game da zaben na bana.

A ganawar INEC da shugabannin jam'iyyun, an bayyana adadin 'yan Najeriyan da zau yi zabe daodai da tsari.

An kuma bayyana sauran shirye-shirye da adadin masu kada kuri'u a kowace jiha a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel