Labaran garkuwa da mutane
Za a ji labari 'Yan sandan reshen jihar Legas sun yi ram da wani mutum mai shekara 36 da zargi mai ban al'ajabi. Nan da kimanin makonni biyu za a koma kotun.
Yanzu muke samun labarin yadda aka sace wani dan takarar majalisar wakilai a matakin jiha a jihar Ribas yayin da ya saura kwanaki uku kacal a yi zabe a kasar.
Wasu 'yan bindiga a jihar Zamfara sun aikata mummunan barna ta hanyar sace mijin wata mata tare da 'ya'yanta hudu a wani yankin jihar Zamfara da ke a Arewa.
Yanzu muke samun labarin yadda wasu 'yan bindiga suka yi bata-kashi da 'yan sanda, inda aka ceto wani dan jairdan da aka sace a makon nan, ranar ta Alhamis.
Rundunar 'yan sanda reshen jihar Zamfara sun lalata wani mafakar yan fashin daji a Zamfara, sun kubutar da mutane 14 da suka shafe sama da watanni biyu a daji.
Wasu tsagerun yan bindiga sun kutsa kai rukunin gidajen Grow homes estate da ke yankin Kubuwa a babban birnin tarayya Abuja, sun yi garkuwa da akalla mazauna 9.
Yan bindiga a Kaduna sun kai hari garuruwan Karimbu-Kahugu a karamar hukumar Lere a Kaduna a safiyar ranar Juma'a inda suka kashe dan fasto tare da sace matarsa
Rundunar yan sandan jihar Zamfara sun yi nasarar kama wani matashi mai suna Thomas Ya'u dan shekara 20 kan zargin garkuwa da mahaifiyarsa ya karbi fansar N30m.
A wani sabon hari da aka kai jihar Kaduna, miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da matar aure, 'ya'yanta biyu da wasu mazauna 9 a ƙauyen Janjala, yankin Kagarko.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari