Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Coci, Sun yi Garkuwa da Mutum 25

Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Coci, Sun yi Garkuwa da Mutum 25

  • Hankula sun tashi yayin da wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne suka kai hari wata majami'a mai suna New Life For All dake karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina
  • An ruwaito yadda masu garkuwa da mutanen su ka yi dirar mikiya a majami'ar gami da tasa keyar masu bauta 25 tare da barin faston majami'ar da raunuka
  • Babban mai taimakawa gwamnan Katsina kan lamurran addinin Kirista ya sanar da yadda jami'an tsaro suke kokarin ganin an saki wadanda aka sace

Katsina - Wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne a safiyar Lahadi, 15 ga watan Janairun 2022, sun kai hari wata majami'a mai suna Life For All da ke karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina, inda su ka yi garkuwa da masu bauta 25, Channels TV ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Yi Garkuwa da Matar Wani Ma'aikacin Kamfanin Mai Na Kasa NNPC

'Yan binidga
Katsina: 'Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Coci, Sun yi Garkuwa da Mutum 25. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Babban mataimaki na musamman ga gwamna Aminu Bello Masari kan lamurran da suka shafi addinin Kirista, Rabaren. ishaya Jurau ne ya bayyana hakan ranar Lahadi.

A cewarsa:

"'Yan bindiga sun kutsa Majami'ar New Life For All ta Jan-Tsauni, Gidan Haruna cikin karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina ranar Lahadi misalin karfe 10:00 na safe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sun yi garkuwa da masu bauta 25 a coci gami da barin faston majami'ar da raunuka yayin da suke tsaka da masu bautar a safiyar yau Lahadi."

A cewarsa, jami'an tsaron jihar suna fafutukar ganin an saki wadanda aka yi garkuwan da su.

Sai dai, binciken da jaridar Leadership tayi ya bayyana yadda aka saki wasu daga cikin wadanda barayin suka sacen.

Kaduna: Direbobi sun rufe babbar hanyar Zaria zuwa Kano

A wani labari na daban, direbobin babbar mota sun rufe babbar hanyar Zaria zuwa Kano duka don fusata da suka yi kan kisan da wani soja yayi wa abokin aikinsu.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Halaka Basarake a Jihar Arewa, Gwamna Ya Kakaba Dokar Zaman Gida

An gano cewa sojan ya halaka direban bayana hatsaniya ta hada su amma babu matakin ladabtarwa da aka dauka a kansa.

Sai dai majiyar gani da ido ta tabbatar da yadda direbobin suka kwashe kusan kwanaki uku sun rufe hanyar amma daga bisani suka sake ta ranar Juma'a da ta gabata.

Legit.ng Hausa ta bi babbar hanyar a ranar Lahadi inda ta tarar da ita lafiya kalau babu cunkoso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel