Katsina
Shugaban ƙasa, Alhaji Muhammadu Buhari, ya faɗa wa jam'iyyar APC cewa haɗin kai ne kaɗai zai kai ta ga nasara a zaɓe mai zuwa, Radda da Jobe sun kai masa ziyara
Wani malamin makaranta a jihar Katsina ya ci amanar abokinsa yayin da ya ba shi gubar bera a Fura da Nono kafin daga bisa ya sace motarsa a wani kango a jihar.
A yau babu asibitocin tarayya a jihohi 15 irinsu Kano, Kaduna, Sokoto, Borno, Akwa-Ibom, Edo, Anambra, Ebonyi. Yanzu kuma gwamnati za ta gina wani a Daura.
Jam'iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben ɗan takararta na gwamna Katsina, Dakta Dikko Radda a karamar hukumar Faskari ranar Litinin 5 ga watan Disamba.
‘Yan bindiga dake yankin dajikan Funtua sun kai farmaki kan masu sallar Isha’i a daren Asabar, sun sace mutane masu yawa. Sun harbe limami tare da raunata wasu.
Sojojin Najeriya sun yi caraf da wasu abokan harkallar 'yan bindiga da ake kyautata zaton sun dauko kudi ne daga gare su. An kama su da kudi N19.5m a mota.
Yan sanda a jihar Katsina sun yi nasarar kama wani mutum dan shekaru 53 wanda ya kware wurin kera wa yan bindiga da sauran batagari rigar sulke na kare harsashi
Aminu Masari, gwamnan jihar Katsina ya bukaci yan Najeriya su tabatar sun zabi Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023 don ya fi sauran yan takarar cancanta
Al’ummar yankin Danmusa da ke jihar Katsina sun shiga unguwannin don zanga-zanga a kan harin yan bindiga da yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyar DPO da kaninsa
Katsina
Samu kari