Yan sanda sun gwabza da wasu yan bindiga a Katsina, sun tura mutum 2 lahira

Yan sanda sun gwabza da wasu yan bindiga a Katsina, sun tura mutum 2 lahira

  • Dakarun yan sanda bisa taimakon yan Bijilanti sun samu nasarar dakile harin yan bindiga a yankin Jibia, Katsina
  • Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya ce bayan musayar wuta da maharan, dakaru sun aika biyu daga ciki lahira
  • Kwamishinan yan sandan Katsina ya yaba da jajircewar Yan Bijilanti da suka taimaka wajen samun nasara

Katsina - Rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ta halaka yan bindiga biyu a ƙoƙarin da take na kawo ƙarshen ayyukan ta'adda a jihar, kuma ta kwato bindigun AK-47.

Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai ranar Litinin a Katsina, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Ya ce yan ta'addan sun gamu da ajalin su ne bayan sun kai farmaki yankin Kahiyal dake ƙauyen Bugaje a ƙaramar hukumar Jibia, jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun kai mummunan hari Sakatariyar karamar hukumar da gwamna ya fito

Taswirar jihar Katsina.
Yan sanda sun gwabza da wasu yan bindiga a Katsina, sun tura mutum 2 lahira Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin yan sandan ya yi bayanin cewa dakaru sun samu nasarar ne awanni bayan samun kiran gaggawa cewa yan ta'adda da yawa ɗauke da Ak-47 sun kai hari yankin.

Yan sanda sun kai ɗauki cikin lokaci

A cewar Gambo Isa, Dakarun yan sanda na sashin yaƙi da garkuwa da mutane bisa jagorancin DPO na Jibia da wasu yan Bijilanti suka kai ɗaukin gaggawa.

Ya ce jami'an tsaron sun tari yan ta'addan a hanyar fita bayan harin, suka yi musayar wuta, suka daƙile mummunan harin, kuma suka sheƙe biyun su.

Leadership ta rahoto Kakakin yan sandan ya ce:

"Dakarun sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane bisa jagorancin DPO na Jibia da wasu Yan Sa'kai suka tari maharan, suka yi musayar wuta, aka samu nasarar tura biyu lahira."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun kutsa har cikin gida sun kashe wani fitaccen Attajiri a Katsina da Azumi

Bayan haka ya miƙa saƙon kwamishinan yan sandan jihar, CP Idris Dauda Dabban, na yabo ga yan Bijilantin da suka ba da gudummuwa wajen samun nasara.

A wani labarin kuma Bayan ɗalibai sun kwashe kwana 56 a gida, Gwamnatin Buhari ta shirya zama da ASUU

Gwamnatin tarayya ta shirya zama don cigaba da tatttauna wa da kungiyar malaman Jami'o'i ASUU yau Litinin.

Ma'aikatar kwadugo da samar da aikin yi tace Dakta Chris Ngige ne da kansa zai jagoranci zama da wakilan ASUU.

Asali: Legit.ng

Online view pixel