Katsina: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Dama

Katsina: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Dama

  • Wasu yan bindiga a kan babura sun kai hari a kasuwar Yantumaki a karamar hukumar Danmusa na Jihar Katsina
  • Yan bindigan sun shiga kasuwar suna harbe-harbe, suka bindige mutum biyar suka sace wayoyi sannan suka sace wasu mutane
  • Kakakin yan sandan Katsina SP Gambo Isah ya tabbatar da harin amma a cewar mutum daya aka kashe yayin da mazauna garin sunce mutum 3 aka kashe

Jihar Katsina - Yan bindiga sun kashe wani treda a kasuwan Yantumaki a karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina a ranar Juma'a.

The Punch ta rahoto cewa yan ta'addan sun kuma raunata yan kasuwa bakwai sannan sun sace mutane da dama da ba a san adadinsu ba yayin harin.

Katsina: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Dama
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kasuwa a Katsina, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Dama. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari a Kaduna, Ana Fargabar Sun Kashe Mutane Da Dama

Yan ta'addan sun kai farmaki a kasuwan ne jim kadan bayan sallar Juma'a.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin, ta ce mutum daya aka kashe

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce mutum daya ne kadai aka kashe.

Ya ce:

"A yau (Juma'a) wasu yan ta'adda a kan babura guda hudu, sun kai hari a sashin yan waya (GSM) na kasuwar Yantumaki suka fara harbe-harbe. Sun harbi mutane shida sun sace wayoyi da yawa.
"Mutum daya ya mutu sauran biyar din suna babban asibitin Danmusa. Daga baya an mayae da wasu cikinsu asibitocin Dutsinma da Katsina. Yanzu komai ya koma yadda ya ke."

Mutanen garin sun ce mutum 3 ne aka kashe

Wasu mazauna garin sun bayyana cewa yan ta'addan sun isa kasuwar ne misalin karfe 3 na rana.

A cewar wasu mazauna garin, yan ta'addan sun kashe yan kasuwa uku, sun raunata bakwai sannan sun tafi da mutane da dama cikin daji.

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

'Yan Ta'adda Sun Sake Kai Hari a Kaduna, Ana Fargabar Sun Kashe Mutane Da Dama

A wani labarin, ana fargabar mutane da dama sun mutu sakamakon harin da yan bindiga suka sake kai wa a wani gari a karamar hukumar Chikun na Jihar Kaduna.

TVC News ta rahoto cewa yan ta'addan masu dimbin yawa sun afka Anguwan Bulus da ke Sabon Tasha misalin karfe 10 na daren ranar Alhamis.

Duk da cewa rundunar yan sandan Jihar Kaduna bata riga ta tabbatar da kai harin ba, an fahimci cewa yan ta'addan sun bude wa mutane wuta a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel