Gwamna Masari ya ayyana gobe Litinin, 11 ga watan Afrilu a matsayin hutu, ya bayyana dalili

Gwamna Masari ya ayyana gobe Litinin, 11 ga watan Afrilu a matsayin hutu, ya bayyana dalili

  • Gwamnatin Katsina ta baiwa ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu izinin hutawa a ranar Litinin 11 ga watan Afrilu
  • Masari ya bayar da wannan hutun ne domin ma’aikata su samu damar jefa kuri’a a zaben kananan hukumomi
  • Sakataren din-din-din na ofishin shugaban ma’aikata, Usman Isyaku, ne ya fitar da sanarwa

Katsina - Jaridar Leadership ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana Litinin, 11 ga watan Afrilu, a matsayin ranar hutun aiki.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayar da wannan hutun ne domin ma’aikata da iyalansu su samu damar kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da za a gudanar.

Gwamna Masari ya ayyana gobe Litinin, 11 ga watan Afrilu a matsayin hutu, ya bayyana dalili
Gwamna Masari ya ayyana gobe Litinin, 11 ga watan Afrilu a matsayin hutu domin zaben kananan hukumomi Hoto: Sahara Reporters
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ofishin shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Isyaku.

Sanarwar wacce aka fitar a ranar Asabar, 9 ga watan Afrilu ta ce hakan zai ba ma’aikatan gwamnati damar komawa mazabarsu domin jefa kuri’a.

Kara karanta wannan

Ziyarar Kaduna: Tinubu ya samu tabarraki daga wajen Sheikh Dahiru Bauchi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bukaci ma’aikata da su yi amfani da damar wajen sauke hakkinsu cikin lumana ta hanyar zabar yan takarar da suka muradi, rahoton Thisday.

Gwamnan Arewa Ya Shawarci Kirista Su Shiga Siyasa Don Dawo Da Martabar Najeriya

A wani labarin, gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom ya bukaci kiristoci su shiga siyasa wanda ya ce zai taimaka a dawo da martabar Najeriya, rahoton Nigerian Tribune.

Da ya ke magana yayin gana wa da mambobin Knight of St. Mulumber, Abuja karkashin jagorancin Sir Michael Awuhe a ranar Juma'a, gwaman ya ce kuskure ne kiristoci su rika yi wa siyasa kallon kazamar wasa.

Ya yi kira ga shugabannin kiristoci su karfafa wa mambobinsu gwiwa su yi rajistan katin zabe da aka yi a yanzu.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

Asali: Legit.ng

Online view pixel