Da dumi-dumi: Sanata mai wakiltan yankin Buhari ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a hukumance

Da dumi-dumi: Sanata mai wakiltan yankin Buhari ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a hukumance

  • Ahmed Babba Kaita, sanata mai wakiltan yankin Katsina ta arewa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa PDP a hukumance
  • Babba-Kaita ya bayar da sanarwar sauya shekar tasa ne a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu, inda hakan ya kawo karshen jita-jita da ake ta yadawa
  • Tun a ranar Talata dai ya ziyarci sakatariyar PDP amma sai ya karyata batun cewa saboda sauya shekar da zai yi ne ya je chan

Katsina - Ahmed Babba Kaita, sanata mai wakiltan yankin Katsina ta arewa, wato mazabar shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.

Premium Times ta rahoto cewa Mista Babba-Kaita ya sanar da cewa ya koma jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) mai adawa, a ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: N100m zamu sayar da Fom din takarar kujerar shugaban kasa, Jam'iyyar APC

Da dumi-dumi: Sanata mai wakiltan yankin Buhari ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a hukumance
Da dumi-dumi: Sanata mai wakiltan yankin Buhari ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a hukumance Hoto: @SalihuAmumini
Asali: Twitter

Sauya shekar nasa ya kawo karshen rade-radin da ake ta yi a gidajen radiyo a Katsina da kuma shafukan soshiyal midiya cewa sanatan zai sauya jam’iyyar siyasa gabannin babban zaben 2023.

A ranar Talata, 19 ga watan Afrilu da rana, Babba-Kaita ya ziyarci sakatariyar PDP a Katsina amma daga jam’iyyar har sanatan sun karyata cewa ya je wajen ne don sauya sheka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa na sauya sheka - Babba-Kaita ya bayyana

A wata sanarwa daga hadimin labaran sanata, Abdulkadir Lawal, Kaita ya ce ya sauya sheka ne saboda shi ba dan siyasa me neman suna bane.

Ya kuma bayyana cewa PDP ce ke wakiltan akidarsa.

Ya ce:

“Sanata Ahmad Babba Kaita bad an siyasa mai neman suna bane. Kyakkyawar wakilcinsa a majalisar dattawan Najeriya abin sha’awa ne ga kowa, kuma yana da tasirin gaske a bangaren samar da ababen more rayuwa da ci gaban jama’a a fadin yankuna uku na jihar. Akwai damar yin fiye da haka.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Tsaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu ci ke raba kan 'ya'yan jam'iyya, Abdullahi Adamu

“Sabon shafin da ke tattare da hukuncinsa na komawa jam’iyyar Peoples’ Democratic Party (PDP) yana wakiltan manufofin, kyakkyawan fata da kuma damar da za ta taimaka wajen samawa mutane romon damokradiyya.”

Sanatan ya zargi gwamnan jihar, Aminu Masari, da kin gudanar da zabukan karamar hukuma tsawon sama da shekaru shida. Ya ce gwamnan ya yi watsi da sauran masu ruwa da tsaki, baya mutunta tushen damokradiyya, sannan ya tsani ba kowa damar gwada bajintarsa a harkokin jam’iyya.

2023: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC ya kaɗu da jin kuɗin fam Miliyan N100m

A wani labarin, dan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, Adamu Garba, ya bayyana kaɗuwarsa ƙarara da jin tsabar kuɗin da jam'iyya ta sanya wa Fam ɗin sha'awar takara.

A yau Laraba yayin taron majalisar koli (NEC), jam'iyya mai mulkin ƙasar nan ta amince da sanya Naira Miliyan N100m a matsayin kudin Fam ɗin tsayawa takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jam’iyyar ADP ta hade da wasu jam’iyyu 16 domin fatattakar APC daga Villa

Da yake tsokaci kan lamarin a shafinsa na dandalin sada zumunta Twitter, Garba, wanda ya nemi takara a 2019, ya rubuta cewa, "Miliyan N100m kuɗin Fam! Lallai."

Asali: Legit.ng

Online view pixel