Zaben kananan hukumomin Katsina: APC ta lallasa PDP, ta lashe dukka kujeru 31

Zaben kananan hukumomin Katsina: APC ta lallasa PDP, ta lashe dukka kujeru 31

  • Jam’iyyar APC ta sake kafa daularta a jihar Katsina bayan ta lashe dukka kujerun ciyamomi 31 a zaben kananan hukumomi da aka yi
  • Sai dai kuma, hukumar zabe ta jihar ta bayyana cewa har yanzu bata samu sakamakon zabe ba a kananan hukumomin Daura da Funtua
  • Ta kuma bayyana cewa wasu matsaloli da suka kunno kai sun tilasta mata soke zabe a karamar hukumar Dutsin-Ma

Katsina - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a kan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) wajen lashe dukka kujeru 31 a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar.

Babban sakataren hukumar zabe ta jihar, Alhaji Lawal Faskari ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu a garin Katsina.

Faskari ya kuma bayyana cewa ba a kammala zabe ba a kananan hukumomin Daura da Funtua, PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta ba APC mamaki, ta lashe kujerun Ciyamomi 21 da Kansiloli 226 a Adamawa

Zaben kananan hukumomin Katsina: APC ta lallasa PDP, ta lashe dukka kujeru 31
Zaben kananan hukumomin Katsina: APC ta lallasa PDP, ta lashe dukka kujeru 31 Hoto: @GovernorMasari
Asali: Twitter

Har ila yau, ya kuma bayyana cewa an soke zabe a karamar hukumar Dutsin-Ma saboda wasu kalubale, yana mai cewa an yi zaben cikin lumana a dukka sauran yankunan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa:

“An yi zaben cikin lumana, kuma akalla jam’iyyun siyasa da aka yiwa rijista 12 ne suka shiga zaben, sai dai a Dutsin-Ma, inda matsaloli suka tilastawa hukumar amfani da sashi na 60 na dokar zaben kananan hukuma ta jihar Katsina, 2002 wajen hana shirin.
“Zuwa yanzu hukumar ta karbi cikakken sakamako daga kananan hukumomi 31, unguwanni 328, tana jiran na Funtua da Daura, yayin da aka soke zabe a Dutsin-Ma.
“Don haka, hukumar na burin sanar da cewa APC ta lashe dukka kujerun Ciyamomi 31 da na kansiloli 328 zuwa yanzu.”

Ya taya wadanda suka yi nasara a zaben murna sannan ya jinjinawa jam’iyyun siyasa kan halin dattako da suka nuna a yayin da bayan zaben, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Matsalolin da Najeriya ke fuskanta alamun daukaka ne, In ji dan majalisa daga arewa

Faskari ya kara da cewa:

“Hukumar KTSIEC na burin nuna godiyarta ga masu zabe da sauran masu ruwa da tsaki, da sauran mutanen jihar kan tarin goyon baya da hadin kai da suka bayar.”

Gwamna Masari ya ayyana gobe Litinin, 11 ga watan Afrilu a matsayin hutu, ya bayyana dalili

Mun kawo a baya cewa Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana Litinin, 11 ga watan Afrilu, a matsayin ranar hutun aiki.

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayar da wannan hutun ne domin ma’aikata da iyalansu su samu damar kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da za a gudanar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ofishin shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Isyaku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel