Babban magana: Dubban 'yan APC da PDP a Katsina sun koma jam'iyyar su Kwankwaso NNPP

Babban magana: Dubban 'yan APC da PDP a Katsina sun koma jam'iyyar su Kwankwaso NNPP

  • Jim kadan bayan kammala zaben kananan hukumomi a jihar Zamfara, 'yan takarar majalisa sun sauya sheka
  • 'Yan takarar biyu da mabiyansu sama da 8000 ne suka karbi takardun shiga jam'iyyar NNPP mai tasowa
  • A jawaban shiga jam'iyyar, 'yan takarar biyu sun bayyana dalilansu na barin jam'iyyunsu na baya; PDP da APC

Jihar Katsina - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, sama da mambobin jam’iyyar APC da PDP 8,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP a jihar Katsina.

Dubban mutanen, wadanda magoya bayan Hon Yazzi Muhammad ne da Hon Al-Amin Yahaya Sani, ‘yan takarar majalisar dokoki ta APC da PDP, sun gabatar da kansu ga shugabancin jam’iyyar NNPP a jihar baki daya.

'Yan siyasar Katsina sun sauya sheka
Shirin 2023: Dubban 'yan APC da PDP Katsina sun koma jam'iyyar su Kwankwaso NNPP | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar Yazzi Muhammad sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ne biyo bayan ganin sakamakon zaben kananan hukumomin da aka kammala wanda ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin mara gaskiya da kishin ci gaban al’umma.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar dokoki 2 sun bada sanarwar sauya-sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP

Al-Amin Yahaya ya ce ya koma jam’iyyar NNPP ne domin tabbatar da burinsa na wakiltar Katsina ta tsakiya a majalisar dokokin jihar, inda ya ce rashin gaskiya na PDP ya sa ya bar jam’iyyar zuwa NNPP.

Da yake karbar ’yan takarar biyu da magoya bayansu, shugaban jam’iyyar NNPP na karamar hukumar Katsina, Umar Usman, ya ba su tabbacin kauna, daidaito da goyon bayan jam’iyyar don ci gaban jihar da kasa baki daya.

Zaben kananan hukumomin Katsina: APC ta lallasa PDP, ta lashe dukka kujeru 31

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a kan jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) wajen lashe dukka kujeru 31 a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar.

Babban sakataren hukumar zabe ta jihar, Alhaji Lawal Faskari ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu a garin Katsina.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Bayan ganawa da gwamnoni, Osinbajo ya gayyaci 'yan majalisun APC

Faskari ya kuma bayyana cewa ba a kammala zabe ba a kananan hukumomin Daura da Funtua, PM News ta rahoto.

Har ila yau, ya kuma bayyana cewa an soke zabe a karamar hukumar Dutsin-Ma saboda wasu kalubale, yana mai cewa an yi zaben cikin lumana a dukka sauran yankunan.

2023: ‘Dan takarar APC ya musanya rade-radin hakura da neman zama Shugaban kasa

A wani labarin, Francis Nwaze wanda ya na cikin masu magana da yawun Dave Umahi, ya yi watsi da jita-jitar cewa gwamnan Ebonyi ya hakura da shiga takara.

Premium Times ta rahoto Mista Francis Nwaze yana cewa Gwamna Dave Umahi yana nan a kan bakarsa na neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

A makon nan rahotanni suka fara yawo cewa Mai girma Dave Umahi ya koma neman tikitin Sanatan kudancin jihar Ebonyi a maimakon na shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jerin ‘yan siyasa 35 da suka fito takara zuwa yanzu, su na hangen kujerar Buhari a Aso Villa

Asali: Legit.ng

Online view pixel