Yan bindiga sun bindige sabon zababben kansilan APC a Katsina, sun yi awon gaba da matansa 2

Yan bindiga sun bindige sabon zababben kansilan APC a Katsina, sun yi awon gaba da matansa 2

  • Yan bindiga sun bindige Alhaji Nasiru Magaji, sabon zababben kansilan unguwar Gozaki da ke karamar hukumar Kafur na jihar Katsina
  • Lamarin ya afku ne a safiyar yau Laraba lokacin da maharan kimanin su 10 suka farmaki gidan marigayin a kan babura
  • Hakazalika maharan sun yi garkuwa da matan mamacin su biyu amma sai suka sako su daga bisani

Katsina - Wani sabon zababben kansila na APC a jihar Katsina ya rasa ransa sakamakon bindige shi da wasu yan bindiga suka yi a wani farmaki da suka kai mahaifarsa a daren Talata har zuwa wayewar garin Laraba.

An kashe kansilan mai suna Alhaji Nasiru Magaji, wanda aka fi sani da Nasiru B.S a garin Gozaki da ke karamar hukumar Kafur ta jihar, rahoton Thisday.

Kara karanta wannan

Sabon hari: ‘Yan bindiga sun budewa jama'a wuta, sun kashe wani malamin sakandare a Zamfara

An harbe marigayin ne a gidansa sannan aka kwashe shi zuwa wani asibiti a garin Malumfashi, inda a nan ne aka tabbatar da mutuwarsa.

Yan bindiga sun kashe sabon zababben kansila a Katsina, sun yi awon gaba da matansa 2
Yan bindiga sun kashe sabon zababben kansila a Katsina, sun yi awon gaba da matansa 2 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Gozaki, Abdullahi Gozaki, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa yan bindigar wadanda yawansu ya kai 10 sun kuma sace matayen marigayin biyu amma sai suka sako su daga baya.

Ya ce:

“Sun kai farmakin ne a safiyar yau (Laraba) da misalin 12:30am, sun kashe kansilan sannan suka sace matayensa biyu amma daga baya sun sako su.”

'Yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisar tarayya a jihar Filato

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga a ranar Talata da daddare sun yi wa tawagar sabon zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa-Bassa, Musa Agah kwanton bauna.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 5 a Hanyarsu Ta Dawowa Daga Ɗaurin Aure

An ce dan majalisar tarayyar da mukarrabansa na dawowa gida ne da misalin karfe 9 na dare a lokacin da lamarin ya faru a kusa da Twin Hill Miango, a karamar hukumar Bassa a jihar Filato.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin ga AIT, hadimin dan majalisar, Moses Maly, wanda suke cikin mota daya lokacin da lamarin ya faru, ya ce matar dan majalisar da ‘ya’yansa biyu su ma suna tare dasu amma duk sun tsere yayin da motarsa ta farfashe da barin harsasai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel