Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

  • Ministan Sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ci gaba da neman goyon bayan al'umma kan kudirin sa na takarar shugaban kasa
  • Gabanin zaben 2023, Amaechi ya kai wa gwamnan jihar Katsina ziyara inda ya bayyana cewa yana son ya jagoranci kasar nan ne duba da kwarewarsa
  • A halin da ake ciki, ministan ya ce zai ci gaba da irin ayyukan da yake yi na alheri a yanzu idan ya zama shugaban kasa a zaben 2023

Jihar Katsina - Rotimi Amaechi, ministan sufuri na Najeriya, ya ce yana da kwarewar da ake bukata na zama shugaban Najeriya a zaben 2023.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa Gwamna Bello Masari na jihar Katsina ziyara, a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Yadda na zama mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya bada labari mai taba zuciya a bidiyo

Amaechi ya bayyana cewa shi kadai ne dan takarar shugaban kasa da ya taba mulkar jihar da ake fama da rikicin ‘yan bindiga.

Burin Amaechi na gaje Buhari
Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara | Hoto: Rt Hon Chibuike R Amaechi
Asali: Facebook

Ministan ya kara da cewa a karkashin jagorancin sa a jihar Ribas an samu raguwar ‘yan tada kayar baya, kana wasu kamfanonin mai sun mayar da hedikwatarsu zuwa jihar.

Shirye-shiryen sa na gaba a siyasa

Ya ce zai maimaita duk nasarorin da ya samu a Ribas a matakin tarayya.

Ministan ya kuma yi amfani da shafinsa na Facebook inda ya yada bidiyon ziyarar tasa ga gwamnan na garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya rubuta cewa:

"Na ziyarci Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari domin jajanta mashi da Masarautar Katsina sakamakon rasuwar Sarkin Sullubawa Hakimin Kaita, Abdulkarim Usman."

A nasa bangaren, Masari ya ce Amaechi na da kyakkyawar damar zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

Kara karanta wannan

Manyan jihohin kudu maso yamma 3 da Osinbajo zai iya rasawa idan ya zama dan takarar APC

Ya muka kare da Buhari balle Osinbajo: Tsokacin lauya ga takarar Osinbajo a 2023

A wani labarin, Festus Ogun, daya daga cikin lauyoyin Najeriya masu tasowa kuma mai fafutukar kare hakkin bil adama, ya yi kira ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da ya manta da batun tsayawa takarar shugabancin kasar nan domin amfanin kasar.

A cewar Ogun, wanda ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da Osinbajo, mataimakin shugaban kasar ya kasance jigo a gwamnatin Buhari, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ya kara da cewa gwamnatin su Osinbajo ta kawo wa Najeriya wahalhalun da ba a taba gani ba, wadanda suka durkusar da kasar a zahiri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel