Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su

  • 'Yan sanda sun yi nasarar sheke'yan ta'adda biyu gami da fatattakar sauran bayan sun yi kokarin garkuwa da wata mata da 'diyarta a Katsina
  • Tsabar luguden wutar da tawagar 'yan sanda da kungiyar 'yan sa kai suka musu ne yasa suka tsere gami da watsi da kayyakin ta'addancin su
  • An ceto matar da diyarta ba tare da wani rauni ba, wanda hakan yasa kwamishinan 'yan sandan jinjinawa namijin kokarin da suka yi

Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta yi nasarar sheke a kalla 'yan ta'adda guda biyu, tare da gano makamansu, kayan sihirce-sihircensu da abubuwa masu fashewa a ranar Alhamis.

Channels TV ta ruwaito cewa, kakakin 'yan sandan, Gambo Isah, ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai a hedkwatar rundunar a Katsina.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6

Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su
Katsina: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 2, sun ceto wasu da aka yi garkuwa da su. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Ya ce, an yi nasarar sheke 'yan ta'addan bayan samun wani kiran gaggawa da rundunar tayi na cewa 'yan bindiga sun kai wa kauyen Tsamiyar Gamzako dake karamar hukumar Kafur na jihar hari, gami da yin garkuwa da wata mata mai shekaru 30 da 'diyarta 'yar watanni 15.

Isah ya bayyana yadda aka sanarwa da tawagar 'yan sanda da kungiyar 'yan sakai, inda suka tare su, tare da dakile harin nasu ta hanyar bude musu wuta, cewar rahoton PM News.

Ya cigaba da bayyana yadda aka ceto wadanda aka yi garkuwan dasu ba tare da wani rauni ba, sannan an gano bindiga kirar AK-47 guda daya da abubuwa masu fashewa guda hudu da bindigogin toka guda shida.

Ya cigaba da bada labarin yadda wasu daga cikin 'yan ta'addan suka ranta a na kare, kakakin 'yan sandan ya ce jami'an tsaro na cigaba da bincikar yankin don da sa ran damko hatsabiban da suka tsere.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Haka zalika, ya kara da cewa, kwamishinan 'yan sandan jihar, Idrisu Dabban Dauda, ya jinjinawa 'yan sanda da 'yan sa kan da suka dakile 'yan ta'addan.

Ya tabbatar wa mutanen yankin cewa 'yan sanda zasu cigaba da farauto 'yan ta'adda har sai an yanke musu hukuncin da ya dace. Saboda haka ne, ya bukacesu da su cigaba da bai wa jami'an tsaro hadin kan da ya da ce ta hanyar basu bayanai masu amfani akan hatsabiban.

Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6

A wani labari na daban, dakarun jami'an hadin guiwa na MNJTF sun halaka mayakan ta'addancin Boko Haram 27 da na ISWAP dake yankin tafkin Chadi a Najeriya, jamhuriyar Nijar da Kamaru, Channels TV ta ruwaito.

A cigaba da ayyukan tsabtace tafkin da dakarun ke yi, sun ceto wasu mata shida da 'yan ta'addan suka yi garkuwa dasu daga jihohin Adamawa, Borno, Gombe da Yobe daga watan Oktoban 2020 zuwa Afirilun 2021.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Dakarun sojin Najeriya sun bindige fitaccen kwamandan IPOB

Asali: Legit.ng

Online view pixel