Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce sai dai ya mutu amma zai yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaro a faɗin jihar da ke Arewa maso Yamma.
Gwamnonin shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya sun cimma matsayar za su haɗa kai wuri ɗaya su tunkari matsalar tsaro da kuma yadda zasu bunƙasa noma.
Gwamna Malam Dikko Umaru Radɗa na jihar Katsina ya kaddamar da Community Watch Corps, sabuwar rundunar tsaro da zata taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhamadu Buhari, Hadi Sirika, ya samu sabon muƙami a gwamnatin jihar Katsina.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa dakarunta sun yi nasarar kuɓutar da mutane 171 da aka yi garkuwa da su a faɗin jihar cikin watanni huɗu.
Labari maras dadi ya zo cewa wasu matasa biyar yan jihar Katsina sun rasa rayukansu kan hanyar zuwa daurin aure daga Katsina zuwa Kano, tuni aka birne su.
Mataimakin shugaban jami'ar tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina ya bayyana dalilin da ya sanya ƴan bindiga suka sace ɗalibai biyar na jami'ar.
Jami'an 'yan sanda sun kwamushe wani da ake zargin ya na bai wa 'yan bindiga bayanan sirri da ya kai ga sace daliban Jami'ar FUDMA a jihar Katsina.
Miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina inda suka yi awon gaba da ɗalibai mata guda biyar.
Katsina
Samu kari