Buhari ya Dira Katsina, Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka

Buhari ya Dira Katsina, Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka

  • Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sauka a jihar Katsina inda zai kaddamar da wasu ayyukan raya kasa na Gwamna Masari
  • Ya dira jihar wurin karfe 10 na dare bayan dawowarsa daga birnin Dakar na kasar Senegal inda ya halarci wani muhimmin taro
  • Zai kaddamar da asibitoci, makarantu, tituna, gadoji da sauransu duk da Gwamna Aminu Masari yayi a fadin jihar

Katsina - Shugaba Muhammadu Buhari ya isa jihar Katsina a ziyarar kwanaki biyu da ya kai domin kaddamar da wasu zababbun ayyuka a fadin mazabun majalisar dattawa a jihar.

Channels TV ta rahoto cewa, jirgin sama dauke da shugaban kasan da tawagarsa ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa Yar'adu da ke Katsina a ranar Laraba wurin karfe 10 na dare inda Gwamna Aminu Masari tare da mukarrabansa suka karbe shi.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Buhari a Katsina
Buhari ya Dira Katsina, Zai Kaddamar da Wasu Manyan Ayyuka. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Buhari ya dira jihar Katsina ne bayan taron da ya halarta a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal.

Ayyukan da zai kaddamar a ranakun Alhamis da Juma'a yawancinsu an yi su ne a tsawon shekaru bakwai da rabi na mulkin Gwamna Masari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun hada da manyan gadojin sama biyu da ke Kofar Kwaya da Kofar Kaura, gyararren babban asibitin Katsina, tashar ruwan famfo ta jihar da sauransu.

Sauran ayyukan da shugaban kasar zai kaddamar a ranar ta biyu sun hada da babban asibiti na Musawa, GDSS Musawa, titin Gora-Makauraci-Mallawama, gyararren titin Sandamu-Baure-Babban Mutuwa tare da na Gurjiya-Sandamu-Karkarku.

Gwamnatin nihar a takardar da ta fitar ranar Laraba, tace Alhamis da Juma'a duk hutu ne domin bai wa ma'aikatan da ke jiha da kananan hukumomin damar tarbar shugaban kasan.

A wata takardar da babban sakataren ma'aikatar al'adu da lamurran cikin gida, Sani Bala Kabomo yasa hannu, yace hutun ranakun bai shafi ma'aikatan tarayya, bankuna da sauran ayyukan da ake bukata a jihar ba.

Kara karanta wannan

Ma'aikata Da Jama'ar Gari Sun Rabauta da Hutun kwana Biyu A Jihar Katsina Dan Zuwan Buhari

Takardar ta kara da kira ga ma'aikatan da hutun ya shafa da jama'a da su fito kwansu da kwarkwata wurin tarbar Buhari da tawagarsa a jihar inda ya shawarci jama'a a jihar da su nuna hali na gari tare da karamcin da aka san su da shi yayin ziyarar.

Buhari zai ziyarci Kano

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Kano a ranakun 30 da 31 ga watan Janairu masu zuwa.

Zai kaddamar da wasu manyan ayyuka da Gwamna Ganduje yayi a fadin jihar a ziyarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel