"Don Allah Ka Taimaka," Malamar Coci Ta Durkusa a kan Gwiwa, Ta Roki Ministan Abuja, Wike

"Don Allah Ka Taimaka," Malamar Coci Ta Durkusa a kan Gwiwa, Ta Roki Ministan Abuja, Wike

  • Malamar coci a Abuja, Fasto Sarah Omakwu ta roki ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya bar wa jama' filin shakatawa na Jabi Lake
  • A wani bidiyo da ta fitar, an ga faston ta durkusa a kan gwiwowinta yayin da take aika wannan dako na roko ga Mista Wike
  • Ta jaddada muhimmancin wurin ga mazauna Abuja, tana mai cewa wurin na da amfani sosai ga rayuwar jama’a ta yau da kullum

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babbar fasto a cocin Family Worship Centre da ke Abuja, Sarah Omakwu, ta roki Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, alfarma kan filin Jabi.

Malamar cocin ta roki Mista Wike da kada ya bai wa kamfanoni masu zaman kansu filin shakatawa na Jabi Lake.

Kara karanta wannan

Jirgin dakon mai ya gamu da iftila'i, an buɗe masa ruwan wuta a mashigar Hormuz

Sarah Omakwu
Malamar coci, Fasto Sarah Omakwu yayin da take rokon Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: Sarah Omakwu
Source: Instagram

Malamar coci ta roki Nyesom Wike

Omakwu ta bayyana wannan roko ne a cikin wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Lahadi, inda aka gan ta ta durkusa a kan mumbari tana rokon ministan.

Faston ta ce:

“Ba zan iya yin fada da Ministan Abuja ba, amma ina roko a matsayina na uwa a wannan kasa cewa kada a bai wa kowa filin Jabi Lake Recreation Centre.”

Muhimmancin filin Jaba ga jama’a

Ta jaddada muhimmancin wurin ga mazauna Abuja, tana mai cewa wurin na da amfani sosai ga rayuwar jama’a ta yau da kullum, cewar rahoton Daily Trust.

“A nan ne mutane ke zuwa motsa jiki, a nan ake kasuwanci, a nan mutane ke haduwa, har ma ana hada aure.
“A nan ake kallon wasanni, matasa na zuwa wurin. Ina rokonka, ya mai girma minista, dan sunanan Allah, dan Allah kada ka sayar da wannan fili ga kowa," in ji ta.

Kara karanta wannan

Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka

Omakwu ta nuna damuwarta

Faston ta kuma nuna damuwa kan yadda wuraren bude ido da na shakawa ke raguwa a Abuja, tana mai ambaton yadda aka takaita shiga wasu wurare kamar kewayen Aso Rock.

Ta kara da cewa:

“Ba zan iya yaki da kai ba, amma ina rokonka da dan Allah, ka taimaka ka bar wannan fili ga jama’a gaba daya.”
Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike yana magana da manema labarai Hoto: @Govwike
Source: Facebook

Wannan kira na zuwa ne bayan gwamnatin Abuja karkashin Nyesom Wike ta rattaba hannu kan yarjejeniya da wasu kamfanoni masu zaman kansu domin mayar da Jabi Lake cibiyar yawon shakatawa da nishadi.

A watan Fabrairu, gwamnatin ta kulla yarjejeniya da kamfanonin Suburban Broadband Limited da Akida Hills Limited domin inganta wurin a wani bangare na kokarin bunkasa harkokin kasuwanci da nishadi a Abuja.

Fasto ya yi maganar zaben 2027

A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Kirista, Fasto Enoch Adeboye ya ce Ubangiji ya riga ya yanke wanda zai zama shugaban kasa na gaba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Lokuta 3 da aka kai wa Donald Trump hari a bindiga za a kashe shi a tarihi

Adeboye ya ce sakamakon zabe ba abu ne da mutane kadai za su iya tantancewa ba, domin nufin Allah shi ne zai tabbata a karshe.

Malamin addinin ya bayyana cewa bai taba hana Kiristoci shiga siyasa ba, amma dole mutane su fahimci cewa Ubangiji ne ke da ikon karshe a harkokin rayuwar bil’adama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262