Dubbannin Mutanen Da Suka Ci Gajiyar SPW Sun Ayyana Goyon Baya Ga Tinubu da Radda

Dubbannin Mutanen Da Suka Ci Gajiyar SPW Sun Ayyana Goyon Baya Ga Tinubu da Radda

  • Katsinawan da suka ci gajiyar shirin SPW sun bayyana Bola Tinubu da Dikko Radda a matsayin zabinsu na 2023
  • A cewar dubbanin ma'aikatan wucin gadin, suna da yakinin yan takarar APC zasu bullo da shirin tallafawa talakawa
  • SPW wani shiri ne da gwamnatin Buhari ta aiwatar da shi wanda yan Najeriya 1000 daga kowace karamar hukuma suka amfana

Katsina - Mutum 34,000 da suka amfana da shirin Special Public Works Scheme (SPW) a jihar Katsina sun ayyana goyon bayan dan takarar shugaban kasana APC, Bola Tinubu, da dan takarar gwamna, Dikko Radda.

A cewarsu, suna da yakinin yan takarar na APC zasu ci gaba da kawo irin wadan nan tsaruka da nufin taimaka wa 'yan Najeriya masu karamin karfi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Dikko Radda da Bola Tinubu.
Dubbannin Mutanen Da Suka Ci Gajiyar SPW Sun Ayyana Goyon Baya Ga Tinubu da Radda Hoto: Dr. Dikko Radda
Asali: Instagram

Shugaban majalisar amintattu na shirin SPW reshen Katsina, Ubale Yusuf Nalado, ya ce wadanda suka amfana da shirin sun dauki wannan matakin ne domin saka wa gwamnatin tarayya karamcin da ta musu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Manyan Kura-Kurai Aka Tafka, Rashin Shugabanci Na Kwarai a Kasar Nan na Shekaru 24 ne ya Tsundumata Halin da Muke Ciki

A kalamansa ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kamar yadda kuke gani, kungiya ce ta magoya bayan siyasa, sun amfana da agajin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kawo musu wanda ya haifar da abu mai kyau a nan Katsina."
"Wannan wata alama ce a fili da ke nuna suna kokarin saka wa Alherin da gwamnatin tarayya ta musu. Ina da tabbacin wannan ne karo na farko a kasar nan."
"Muna batu ne na wadanda suka amfana dubu 34, dubu daya daga kowace karamar hukumar 34 a Katsina, wannan a hukumance kenan amma idan muka kalle su ta wani bangaren, kowanensu yana da iyali."

A nasa jawabin shugaban ma'aikatan wucin gadi na SPW reshen Katsina, Salim Usman, ya bayyana kwarin guiwarsa cewa Tinubu da Radda suna da gogewar gina Najeriya da Katsina.

Haka zalika shugabar matan SPW, Hajiya Binta Abdullahi, ta sha alwashin jawo hankalin mutane su marawa 'yan takarar jam'iyyar APC baya a kowane mataki.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Legit.ng Hausa ta ji ta bakin wasu daga cikin mutanen da suka amfani da SPW a jihar Katsina, inda suka ce sun ɗauka shirin ya daɗe da wucewa.

Wani magidanci, Nura Aliyu, yace tabbas tsarin SPW ya taimaka masa kuma yana gode wa gwamnatin Buhari domin zai iya cewa har yanzun yana amfana.

"Eh na samu SPW, kuma nasan cewa muna da shugabanni a wancan lokacin amma ban ɗauka har yanzu suna nan ba saboda an jima da gama aikin. Ina gode wa gwamnati game da tallafin."

A nasa ra'ayin, Jabir Abubakar, yace yana tare da wannan matakin duk da ba'a tuntube shi ba gabanin yanke hukunci.

"Ina ga saka alkairi yana da kyau, ina gode ma Allah ina gode wa wannan gwamnatin, da wannan kudin na kara a yar sana'ata ta Caji, abu kamar wasa na ɗaga fiye da baya."

"Ina tare da wannan matakin na su, zan zabi Dikko Radda a Katsina da izinin Allah," inji shi.

Kara karanta wannan

2023: Ana Gan da Zabe, Bola Tinubu Ya Gamu da Babbar Matsala a Jihar Shugaba Buhari

Wani Bakatsinen kuma da ake kira da Malam Habu cewa ya yi ba wanda zai tilasta masa ya zabi wanda bai niyya ba.

A cewarsa, yana da mutanen da yake so kuma zai zaɓa, wasu a APC wasu da PDP kuma ba zai sauka daga matakinsa na zaben cancanta ba.

Jam'iyyar LP Ce Babban Kalubalen Mu a Shiyyar Kudu Maso Gabas, Bukola Saraki

A wani labarin kuma Tsohon shugaban majalisar Dattawa, Bukola Saraki, yace Atiku ka iya shan kaye a shiyyoyin Najeriya biyu

Tsohon gwamnan jihar Kwara yace jam'iyyar PDP na da yakin samun galaba a shiyyoyin Najeriya guda hudu a zaben watan Fabrairu.

Abubakar Bukola Saraki na daya daga cikin yan takarar da suka fafata a zaben fidda gwanin PDP amma suka sha kasa a hannun Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel