Ikon Allah ne Yasa Na Tsallake Yakin Basasa, Shugaba Buhari

Ikon Allah ne Yasa Na Tsallake Yakin Basasa, Shugaba Buhari

  • Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yace ya ga mace-mace masu tarin yawa a yayin yakin basasar Najeriya da aka yi a daga 1967 zuwa 1970
  • Ya sanar da cewa, kasancewarsa shugaban kasa yanzu haka duk cikin iko ne da rahamar Allah, ganin irin ramukan mutuwa da ya tsallake
  • Shugaban kasan yace gadoji masu yawa sun tashi da bam kafin zuwansa ko bayan ya bar wurinsu, Allah ne ke shirya kaddara a rayuwa

Katsina - Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace tsallake yakin basasan Najeriya da yayi tsakanin 1967 zuwa 1970 kawai zai ce ikon Allah ne.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, a yayin jawabi ranar Juma'a yayin da ya ziyarci Faruk Umar Faruk, Sarkin Daura, bayan ya kaddamar da wasu ayyuka a Katsina, Buhari yace ya ga mace-mace masu tarin yawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule: Jajiberin 'Dana Zai Rasu, Na Dinga Rarrashin Mahaifin da ya Rasa Yara 9 da Shanu 70 a Tashin Bam din Nasarawa

Baba Buhari
Ikon Allah ne Yasa Na Tsallake Yakin Basasa, Shugaba Buhari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Wannan damar bautawa kasar ta zo ne daga Allah. Dukkan fadin duniya, an san Najeriya da banbance-banbance, tana da addinai da al'adu."

- Takardar da Femi Adesina ya fitar ta bayyana hakan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An kuma san mu da yawan al'umma inda mu ke da miliyoyin jama'a. A matsayin shugaban kasar Najeriya a wannan lokacin, zuwa na Dauar iko ne da rahamar Allah.
"Na sanar da Gwamna Aminu Bello Masari labarin yadda na bar Daura na shiga aikin soja. Haka Allah ya tsara. Muna da zabuka a rayuwa amma daga karshe kaddarar Allah ce za ta bayyana.
"Gadoji da yawa an saka musu bam sun tashi kafin mu isa wurin, ko kuma bayan mun tsallake. Na isa wasu wuraren inda na ga gawawwakin abokan aikina da muke yakin tare. Ina raye ne yau saboda ikon Allah."

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addinin Kirista Ya Fada Wa Yan Najeriya Irin Yan Takarar Da Zama Dole A Kauracewa

Shugaban kasan ya kammala ziyarar kwanaki biyu da ya kai jiharsa ta Katsina a ranar Juma'a.

Ayyukan da ya kaddamar a ranar Juma'a suna hada da babban asibitin Musawa, makarantar gwamnati ta Musawa, titin Gora zuwa Makauraci zuwa Malamawa, Sandamu zuwa Baure zuwa Babban Mutum da Gurjiya zuwa Sandamu zuwa Karkarku.

'Yan sandan sun sanar da rufe wasu tituna na wuci-gadi a Katsina

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun sanar da rufe wasu tituna a fadin jihar na wucin-gadi saboda zuwan shugaban kasa Buhari.

Sun roki jama'a da su kiyaye ba tare da sun karya doke ba saboda a samu ziyarar ta tafi lafiya kalau babu cunkoson tituna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel