Fusatattun Matasa Sun Balle Zanga-zanga Jim Kadan Bayan Buhari ya Kaddamar da Gadar Sama a Katsina

Fusatattun Matasa Sun Balle Zanga-zanga Jim Kadan Bayan Buhari ya Kaddamar da Gadar Sama a Katsina

  • Fusatattun matasa a kwaryar birnin Katsina sun dinga ihun bamu yi, tare da jifan jami'an tsaro da motocin APC jim kadan bayan wucewar Buhari
  • Matasan basu tsaya nan ba, sun dinga kone-kone a titin da Buhari ya kaddamar wanda ke hade da gadar sama ta Kofar Kaura
  • Tuni jami'an tsaro suka yi kansu tare da banka musu barkonon tsohuwa, lamarin da yasa suka watse sannan zaman lafiya ya dawo yankin

Katsina - Wasu matasa a birnin Katsina sun balle zanga-zanga a jihar a ranar Lahadi inda suka dinga kone-kone a tituna.

Zanga-zangar ta fara ne jim kadan bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da gadar sama ta Kofar Kaura wacce aka kamma a birnin Katsina.

Matasa a Katsina
Fusatattun Matasa Sun Balle Zanga-zanga Jim Kadan Bayan Buhari ya Kaddamar da Gadar Sama a Katsina. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Wani ganau ya sanar da jaridar Leadership cewa bayan Shugaban kasan ya bar yankin Kofar Kaura da ke babban birnin, fusatattun matasan sun fara hada wuta kan sabon titin inda suka dinga ihun:

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari, Sun Harbawa Mutane Bama-Baman Roka a Jihar Zamfara

"Bamu yi, Bamu yi"

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

a Hausa.

Kamar yadda yace:

"Suna na Mustapha Muhammad Boss, bayan shugaban kasa Buhari ya kaddamar da gadar saman, wasu jama'a sun bayyana suna ihun "Bamu yi" inda suka dinga jifan jam'ian tsaro da motocin APc tare da kona tayoyi.

"A saboda wannan dalilin, mun yanke hukuncin rufe shagunanmu. Wannan abu bai dace ba kuma bai kamata ba."

Sai dai, jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa wanda a halin yanzu komai ya lafa yayin da shugaban kasan ya garzaya sauran yankunan jihar domin kaddamar da wasu ayyukan.

Legit.ng Hausa ta tuntubi wani matashi da ke karatu a jami'ar Alkalam ta garin Katsina kuma mazaunin wurin gidan Sarki a Katsina, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Matashin mai suna Sa'eed yace:

"Tabbas lamarin ya faru a nan Kofar Kaura, amma hanzarin da jami'an tsaro suka yi dakile shi ne yasa bai yi yawa ba. Kuma dama can ba shiryayyar zanga-zanga bace.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Kotu ta Baiwa DSS Muhimmin Umarni kan Tukur Mamu, Hadimin Gumi da Ake Zargi da Taimakon 'Yan Bindiga

"Kawai sun so tayar da ita kuma tayi kamari ne lokacin amma Allah ya takaita."

'Yan sanda sun rufe wasu titunan Katsina

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da rufe wasu manyan titunan jihar a shirin ziyarar da Buhari ya kai na tsawon kwanaki biyu.

Ta sanar da sunayen titunan tare da kira ga jama'ar jihar da su yi biyayya domin kada a samu cunkoso yayin ziyarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel