An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

  • Peter Obi ya bada labarin yadda aka auka masa da duwatsu da ya je yawon yakin zabe a garin Katsina
  • Wani jawabi ta bakin sashen yada labaran kwamitin kamfe ya ce an kai harin ne a yammacin Litinin
  • Diran Onifade ya ce ‘yan adawan Arewa maso yamma ne suka razana da yadda Obi yake karbuwa

Katsina - Peter Obi mai neman zama shugaban kasa ya bada labarin yadda aka kai wa tawagarsa hari a lokacin da suka ziyarci jihar Katsina.

A yammacin Talata, Daily Trust ta rahoto ‘dan takaran kujerar shugabancin Najeriya a jam’iyyar LP yana cewa an kai masa hari a wajen kamfe.

A wani jawabi da ya fitar ta bakin Diran Onifade, ‘dan takaran ya yi Allah-wadai da abin ya faru da shi da mutanensa da suka je taron siyasa jiya.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku Abubakar Zai Bi Wajen Dankara Tinubu da Peter Obi da Kasa Inji PDP PCC

Shugaban sashen yada labaran kwamitin yakin neman zaben Obi/Datti ‘yan iskan gari sun auka masu da duwatsu ne a kan hanyar zuwa filin jirgi.

Jawabin Diran Onifade

“’Dan takaranmu ya hadu da mata a wajen taro, daga nan sai ya halarci gangami a filin wasa na Muhammad Dikko, aka tashi lafiya kalau.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma a kan hanyarsa ta zuwa filin tashi da saukar jirgin sama, sai wasu ‘yan iskan-gari suka kai wa motar ‘dan takaranmu hari da duwatsu.

‘Dan Takarar Shugaban Kasa
Taron LP a Katsina Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Sun aukawa bangaren kujerar direba, a dalilin haka suka yi wa motar illa sosai.

- Diran Onifade

Abin da rahoton Blueprint ya nuna, an taki sa'a domin kuwa ‘dan takaran na 2023 da duk abokan tafiyarsa ba su samu wani rauni a dalilin hakan ba.

Duwatsu a wajen filin wasa

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Onifade ya kara da cewa an samu wasu ‘yan iskan da suka rutsa su da duwatsu a wajen filin wasan, hakan ya jawo lalata motocin kamfe da-dama.

A cewar kwamitin yakin zaben, wasu ‘yan siyasa da suke tunanin LP ba ta da karfi a Arewa maso yamma ne suka tsorata da irin farin jinin Obi a yankin.

A karshen jawabin, kwamitin ya yabawa Katsinawan da suka nunawa ‘dan takaran na LP kauna, sannan aka bukaci jami’an tsaro su binciki lamarin.

Rikicin cikin gida a LP

Ku na da labarin yadda Jam’iyyar adawa ta LP ta shiga rudani a gabar yakin neman zaben shugaban kasa a jihar Kano saboda sabanin da aka samu.

Bashir I. Bashir, Mohammed Zarewa, Balarabe Wakili da Idris Dambazau sun kauracewa Peter Obi da ya je kamfe saboda rikicin da ake yi a LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel