Shugaba Tinubu Ya Umarci Tsohon Gwamna, Ayade Ya Hakura da Neman Takara a 2027

Shugaba Tinubu Ya Umarci Tsohon Gwamna, Ayade Ya Hakura da Neman Takara a 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade ya janye daga takarar sanata a zaben 2027 bayan ganawa da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Ayade ya tabbatar da cewa Tinubu ya nemi ya janye kuma ya amince duk da cewa bai ji dadin matakin da shugaban kasa ya dauka ba
  • Ya tuna gudummuwar da ya bayar wajen kafa jam'iyyar APC a yankin Kudu maso Kudu, inda ya ce shi ne gwamnan jam'iyyar na farko

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bukace shi da ya janye daga neman takarar sanata a APC.

Ben Ayade dai ya nuna sha'awar neman tikitin jam'iyyar APC na takarar kujerar sanata mai wakiltar Cross River ta Arewa a babban zaben 2027, amma daga bisani ya janye.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya musanta fitowa takarar shugaban kasa a inuwar ADC

Ben Ayade.
Tsohon gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade yana jawabi a wurin taroa lokacin yana kan mulki Hoto: Ben Ayade
Source: Facebook

Abin da Tinubu ya nema daga Ben Ayade

A rahoton da Daily Trust ta wallafa, tsohon gwamnan ya ce Tinubu da kansa ya bukaci ya janye daga takarar sanatan.

Ayade ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce ya dauki matakin janyewa bayan wata ganawar da ya yi da shugaban kasar a Abuja.

“An gayyace ni zuwa Abuja domin wata muhimmiyar ganawa da shugaban kasa. Bayan abubuwan da suka biyo baya, shugaban kasa ya bukace ni da in dakatar da burina na takarar sanata.
"Na amince da bukatarsa duk da cewa ina cikin bakin ciki da radadin abin da ya faru," in ji Ben Ayade.

Ayade ya nuna rashin jin dadinsa

Tsohon gwamnan ya nuna rashin jin dadi kan lamarin, yana mai cewa mai yiwuwa shugaban kasa bai samu cikakken bayani kan halin siyasar jihar Cross River ba.

Kara karanta wannan

A karshe, Gwamnan Bauchi zai sauya sheka, ya fida kujerar da zai nema a 2027

Ya ce mutanen da suka ci gajiyar wannan mataki su ne wadanda suka taba adawa da shi da jam’iyyar APC, musamman kan batun tikitin Musulmi-Musulmi.

Ayade ya kuma zargi wasu daga cikin su da hannu a tashin hankali da aka samu a lokacin zaben 2023, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yaka magana a taron Majalisar Zartarwa a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ayade ya tuna gudummuwarsa ga APC

Ya tunatar da shugaban kasa rawar da ya taka wajen kafa APC a yankin Kudu maso Kudu, yana mai cewa shi ne gwamnan APC na farko a yankin.

“Na yi aiki tukuru domin gina jam’iyyar APC, inda muka samu kuri’u sama da 40,000 a zaben shugaban kasa fiye da PDP, karo na farko a tarihin jihar.”

Duk da haka, Ayade ya ce a shirye yake ya ci gaba da aiki tare da shugaban kasa da gwamnatin jihar domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a idan har wannan mataki zai ci gaba da aiki.

Tsohon gwamnan Cross River ya shiga ADC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Cross River, Donald Duke ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa jam'iyyar ADC a birnin Kalaba.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya bayyana kuri'un da Tinubu zai samu a Kaduna a zaben 2027

An yi wa Duke rajistar zama mamba na ADC a gunduma ta 5 da ke karamar hukumar birnin Kalaba, inda ya karbi katin jam'iyya a gaban dandazon magoya bayansa.

Tsohon gwamnan ya shiga ADC domin hada kai da manyan jagororin adawa irinsu tsohon mataimakin shugaban kasa , Atiku Abubakar da nufin kayar da APC s zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262