Ba'a yiwa Buhari Ihu da jifar Shaidan a Katsina ba, mun kama masu tada tarzoma 8: Hukumar Yan Sanda

Ba'a yiwa Buhari Ihu da jifar Shaidan a Katsina ba, mun kama masu tada tarzoma 8: Hukumar Yan Sanda

  • Kakakin hukumar yan sandan jihar Katsina ya karyata rahotannin cewa an kunyata Buhari a Katsina
  • Rahotanni da bidiyoyi sun yadu cewa yara sun yi shugaban kasan ihun bamaso da jifa da duwatsu
  • Hukumar tace masu satar waya ne suka yi amfani da kananan yara wajen tayar da tarzoma

Katsina - Hukumar yan sandan jihar Katsina sun damke wasu matasa takwas kan zargin tada tarzoma yayinda Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara jiharsa ta Katsina.

Buhari ya kai ziyarar kwana biyu jihar Katsina domin kaddamar da wasu ayyuka.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Gambo Isah, a ranar Juma'a yace bayan shugaban kasa ya kaddamar da titin kasan Kofar Kaura, sun samu labarin cewa wasu kauraye daga Sabuwar Unguwa na fada kuma suka fara sace wayoyin mutane.

Kara karanta wannan

Iko da Rahamar Allah ce Tasa Nake Raye, Na ga Mutuwa a Yakin Basasar Najeriya, Shugaba Buhari

Ya ce hukumar ta gudanar da bincike inda ta gani Kaurayen sun fi amfani da yara wajen jifan motocin jami'an gwamnati da aka tura kama kaurayen.

Gambo ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Juma'a, rahoton ChannelsTV.

Buharo
Ba'a yiwa Buhari Ihu da jifar Shaidan a Katsina ba, mun kama masu tada tarzoma 8: Hukumar Yan Sanda Hoto: Katsina
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba'a yiwa Buhari jifar shaidan ba

Hukumar ta yi watsi da maganar cewa an yiwa Shugaba Buhari jifar shaidan a Katsina.

Gambo yace bidiyoyin da suka yadu a kafafen sada zumunta dake nuna ana yiwa Buhari ishun bamaso na bogi ne yayinda yake kaddamar da gadar Kofar Kaura ranar Alhamis.

Yace Shugaba Buhari ya kaddamar da dukkan ayyukan kuma al'ummar jihar sun tarbesa cikin farin ciki da annashwa.

Saboda haka hukumar na kira da jama'a suyi watsi da bidiyoyin da aka wallafa, a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel