Masarautar Katsina Ta Sake Tuɓe Rawanin Basarake Da Ke Haɗa Baki Da Ƴan Ta'adda

Masarautar Katsina Ta Sake Tuɓe Rawanin Basarake Da Ke Haɗa Baki Da Ƴan Ta'adda

  • Masarautar Katsina ta kori Makaman Katsina, hakimin Bakori, Idris Sule Idris, kan zarginsa da hannu a ta'addanci
  • Korar da aka yi wa Idris Sule Idris na zuwa ne bayan kwamitin da gwamnatin jiha ta kafa don yin bincike ta same shi da laifi bayan mutanensa sun yi korafi
  • A baya, gwamnatin na Katsina ta taba korar Sarkin Pawan Katsina, hakimin Kankara, Yusuf Lawal, shima kan alaka da ta'addanci

Jihar Katsina - Masarautar Katsina ta tabbatar da korar babban hakimi, Makaman Katsina, hakimin Bakori, Idris Sule Idris, kan zargin yana taimakawa da hannu a ta'addanci a yankinsa, rahoton Daily Trust.

Korar tasa na cikin wani wasika ne mai kwanan wata na 19 ga watan Janairun 2023, dauke da sa hannun Kauran Katsina, hakimin Rimi, Aminu Nuhu Abdulkadir, wanda mai nada sarki ne kuma babban mamba na masarautar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

Katsina Map
Masarautar Katsina Ta Sake Tube Rawanin Hakimi 'Mai Taimakawa 'Yan Ta'adda'. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasikar ta ce an kori Makama ne bayan kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa ta same shi da laifin aikata tuhume-tuhumen da mutanensa suka yi masa.

Wani sashi na wasikar ta ce:

"Biyo bayan wasikar da masarauta ta samu daga ofishin sakataren gwamnatin jiha mai lamba da SEC/54/Vol. VI/1416, inda mai girma gwamna ya tabbatar da zargin da ake maka gaskiya ne.
"Zargin abin da aka maka sun janyo rashin zaman lafiya a yankin ka. Don haka, masarautar tana son sanar da kai cewa an sallame ka daga aikinka a matsayin Makaman Katsina, Hakimin Bakori."

Mai magana da yawun masarautar ya tabbatar da korar Makaman Katsina

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun masarautar Katsina, Ibrahim Bindawa ya tabbatar da korar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Katsina: An Yi Nasarar Kubutar da Daya Daga Cikin Mutanen da Yan Bindiga Suka Sace a Wajen Bauta

Ya ce:

"Eh, gaskiya ne."

Ba wannan bane karo na farko da aka korar masu sarautan gargajiya da ke ta alaka da yan ta'adda.

A shekarar 2021, masarautar Katsina ta kori Sarkin Pawan Katsina, hakimin Kankara, Yusuf Lawal, kan zarginsa da tallafawa yan ta'adda.

Kotun Kolin Najeriya Ta Tube Rawanin Basarake A Cross Rivers

A wani rahoton, kun ji cewa kotun koli ta tube rawanin Edidem Ekpo Okon Abasi Otu V, mai sarautar Obong na Calabar.

A cewar Daily Trust, mai shari'a Mohammed Lawal Garba yayin yanke hukuncin ya umurci masu nada sarakuna su fara bin hanyar nada wani Obong na Calabar don maye gurbin Edidem.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164