Katsina: 'Yan Sanda Sun Rufe Titunan Jihar Saboda Ziyarar Buhari

Katsina: 'Yan Sanda Sun Rufe Titunan Jihar Saboda Ziyarar Buhari

  • Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar da rufe wasu muhimman tituna a fadin jihar saboda ziyarar da Shugaba Buhari ya kai jihar
  • Titunan da aka rufe na wucin gadi sun hada da Hanyar IBB, Kofar Kaura, shatale-talen kamfanin karfe, shatale-talen Alkalam zuwa UMYUK
  • Sun yi kira ga jama'a da su bayar da hadin kai tare da kiyaye dokokin domin gujewa cunkoson ababen hawa yayin ziyarar

Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina a daren Laraba ta sanar da rufe wasu titunan jihar na wucin-gadi a kwanaki biyun ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar.

Baba Buhari
Katsina: 'Yan Sanda Sun Rufe Titunan Jihar Saboda Ziyarar Buhari. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Ziyarar za ta fara aiki ne daga ranar Laraba, 26 ga watan Janairun 2023 zuwa 27 ga watan bayan isarsa jihar a daren Laraba.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, titunan da lamarin zai shafa sun hada da duk titunan da ke wuraren da Shugaban kasan zai kaddamar da wasu ayyuka a yayin ziyarar tasa.

Kara karanta wannan

Katsina: Buhari ya Isa Jihar Katsina Daga Dawowarsa Senegal, Gwamna Masari da Ayarinsa Sun Masa Tarbar Karamci

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata takardar da kakakin rundunar, Gambo Isa ya fitar tace:

"Rundunar 'yan sandan jihar Katsina tana sanar da jama'a cewa shugaba Muhammadu Buhari kuma babban kwamandan sojin Najeriya zai sauka a jihar a ziyarar aiki domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar tayi.
"A saboda haka, wadannan hanyoyin da za a lissafo za a rufe su na wucin-gadi daga karfe 8 na safe zuwa 12 a ranar 26 zuwa 27 ga watan Janairun 2023.
"Hanyar IBB, Kofar Kaura, shatale-talen kamfanin karfe, shatale-talen Alkalam zuwa jami'ar Umaru Musa, gadar kasa ta gidan ruwa na Kofar Kaura.
“A ranar 27 ga watan Janairun 2023, titin Dayi zuwa Malumfashi za a rufe shi na wucin-gadi.
"Rundunar tana kira ga ma'abota amfani da titunan da su bi wasu titunan domin gujewa cunkoson hanya.
"Kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina, CP Shehu Umar Nafada, hukumar kula da lamurran 'yan sanda ta na rokon jama'ar jihar Katsina da su hada kai da hukumomin tsaro domin samun nasarar wannan ziyarar ba tare da wani matsala ba."

Kara karanta wannan

Dan takarar gwamnan PDP ya rasu, wa zai maye gurbinsa? Ga abin da doka ta tanada

Buhari ya isa jihar Katsina cikin daren Laraba

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira jihar Katsina daga dawowarsa Najeriya daga taron da ya halarta a birnin Dakar na kasar Senegal.

Wurin karfe 10 na daren Laraba Buhari ya sauak a filin suaka da tashin jiragen sama na Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina inda Gwamna Masari da tawagarsa suka karbe sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel