Jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana kudirin da yake da shi kafin ya bar mulki. Ya ce ya shirya barin jihar fiye da yadda ya same ta.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da mutuwar wani daga cikin hatsabiban 'yan bindiga da yake kiran kansa da Shekau a kwanton-bauna a jihar Kaduna.
Kwamishinonin da suka yi aiki a karkashin tsohuwar gwamnatin jihar Kaduna sun yi zargin cewa hukumar ICPC da kotu za su kwace kadarorin wasu bayin Allah.
Yan bindiga sun hallaka babban limamin cocin katolika bayan sun yi garkuwa da shi ranar Talata 4 ga watan Maris a yankin ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Babbar kotun tarayya mai zamanta a Kaduna ta sahale wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kwato wasu kudi da ake zargin an boye a lokacin Nasir El-Rufa'i.
Kungiyar SOKAPU ta sake daura damara don samun jihar Gurara, tana tattaunawa da mahukunta, tana mai cewa jihar za ta iya dogara da kanta idan an ƙirƙire ta.
A yau Talata 4 ga watan Maris, 2025 dan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, da Ministan Matasa, Ayodele Olawande, sun kai ziyara ta gidan Muhammadu Buhari, a Kaduna.
Rundunar 'yan sandan kasar mam ta tabbatar da cewa an samu sakaci daga wasu daga cikin jami'anta, wanda ya yi sanadiyyar batan dubban bindigun da gwamnati ta samar.
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta zuba idanu wasu tsirarun 'yan siyasa suna kokarin jefa rayuwar jama'a a masifa ba.
Jihar Kaduna
Samu kari