Daga Shigarsa APC, Shehu Sani Ya Fara Kalamai kan Takarar Uba Sani a 2027
- Sanata Shehu Sani ya nuna goyon bayansa ga takarar Uba Sani domin ci gaba da zama gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2027
- Tsohon sanatan ya bayyana cewa zai so a zaɓen 2027 ya samu tikitin takara domin komawa majalisar dattawa
- Shehu Sani ya yabi salon mulkin Uba Sani a Kaduna, inda ya bayyana cewa ya kawo ci gaba fiye da gwamnatin da ta gabace shi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Tsohon sanata kuma mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Sanata Shehu Sani, ya bayyana muradin da yake da shi a siyasance kan zaɓen 2027.
Shehu Sani ya bayyana cewa babban muradin da yake da shi a siyasance a shekarar 2027 shi ne ganin Gwamna Uba Sani na Kaduna ya samu damar yin wa’adi na biyu.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Shehu Sani, wanda kwanan nan ya koma jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani zai goyi bayan Uba Sani a 2027
Shehu Sani ya bayyana cewa zai yi farin ciki idan ya samu tikitin yin takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya a 2027.
“Duba da tsarin siyasar jihar Kaduna, idan na samu tikitin komawa majalisar dattawa a 2027, hakan zai faranta min rai. Amma idan hakan bai samu ba, zan ci gaba da jin daɗi matuƙar mun tabbatar da sake zaɓen Uba Sani a matsayin gwamna."
“Ina matuƙar farin ciki da yadda Kaduna ta kuɓuta daga wanda ya azabtar da ita a siyasance. Wannan ne dalilin da ya sa mu da dama da muka bar APC muka koma PDP, muka yanke shawarar komawa APC."
- Shehu Sani
Ya ba ƴan siyasa shawara
Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisar dattawa ta takwas, ya bayyana cewa mulki abu ne mai wucewa, don haka ya shawarci masu riƙe da madafun iko su rika kyautatawa jama’a.
“Idan Allah Ya ba ka mulki, ka yi amfani da shi don kawo ci gaba ga talakawa. Amma idan ka fara wulakanta mutane, kana kama su ba bisa ƙa’ida ba, kana tayar da zaune tsaye, wata rana mulkin zai ƙare."
- Shehu Sani
Tsohon sanatan ya ce Kaduna ba ta taɓa samun mulki mara inganci ba kamar na shekarun 2015 zuwa 2023 ba, inda ya jaddada cewa abubuwa da dama sun tafi ba daidai ba a jihar.
A cewarsa, rabuwar kai tsakanin Musulmin Arewa da Kiristocin Kudancin jihar ya haddasa matsalolin tsaro, ta’addanci, da sauran ƙalubalen da suka hana ci gaban jihar.
"A Birnin Gwari, manoma sun fara komawa gonakinsu, inda a da sai sun biya ƴan ta’adda miliyoyin naira kafin su noma gonarsu."
“Kodayake ba a cimma dukkan manufofin gwamnati ba, an samu ci gaba mai kyau idan aka kwatanta da baya."
“Tun da Uba Sani ya hau mulki a matsayin gwamna, abubuwa sun inganta sosai. Ba ma jin labarin sace-sacen jama’a da yawa a Kaduna kamar a baya."

Kara karanta wannan
Kudirin kirkiro ƙarin jiha 1 a Najeriya ya samu goyon baya, Sanata Kalu ya jero dalilai
- Shehu Sani
Shehu Sani ya faɗi dalilin komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bayyana dalilin komawarsa zuwa jam'iyyar APC.
Shehu Sani ya bayyana cewa tun da farko wasu dalilai ne suka sanya ya bar APC, amma a yanzu waɗannan dalilan sun kau, shiyasa ya dawo jam'iyyar.
Asali: Legit.ng