Abubuwan da Suka Jawo El Rufai Ya Yi Sallama da APC, Ya Burma Jam'iyyar SDP

Abubuwan da Suka Jawo El Rufai Ya Yi Sallama da APC, Ya Burma Jam'iyyar SDP

A ranar Litinin, 10 ga watan Maris ne tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar APC bayan ya shafe lokaci yana takun saka da gwamnati.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam’iyyar APC bisa dalilai da ake ganin sun shafi siyasa, sabani da shugabannin APC da mayar da shi saniyar ware.

Kafin ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar, an ji yadda abubuwa da dama da ba su yi wa tsohon gwamnan dadi ba su na bayyana.

Nasir
Wasu dalilai da dama ne suka tunzura El-Rufa'i ya fice daga APC Hoto: @BashirElRufai
Asali: Twitter

Legit ta tattaro wasu daga cikin wadannan abubuwa da su ka hada da;

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. El-Rufa'i ya rasa kujerar Minista

Daya daga cikin manyan dalilan da ake zaton sun sa Nasir El-Rufai ya yi fatali da APC shi ne gazawarsa wajen samun mukami a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Daga sauya sheka, El Rufa'i ya fadi yadda zai jawo rugujewar APC a Najeriya

Bayan an nada shi a cikin jerin ministocin da shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisar tarayya, majalisar ta ki amincewa da shi bayan an jinkirta tantancewarsa.

Dama can tsohon ministan ya nuna bai sha'awar kujerar, amma ana zargin watsi da shawarar nada Jafar Ibrahim Sani ya kara damalamla alakar da ke tsakani.

Amma a hirarsa da Arise TV, El-Rufa'i ya ce ba wai majalisa ce ta ki amincewa da nadinsa ba, shugaba Bola Tinubu ne da kansa ya sauya shawara.

2. El-Rufa'i ya samu sabani da gwamnatin Kaduna

An fara ganin hamayyar siyasa karara tsakanin El-Rufa'i da gwamnan Kaduna mai ci, Uba Sani bayan sun fara musayar kalamai.

El-Rufa'i
El-Rufa'i ya fara takun saka da gwamnatin Kaduna Hoto: Nasir El-Rufa'i/Uba Sani
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa yadda Nasir El-Rufa'i ya zargi gwamnan Kaduna da Mashawarcin Tinubu a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu sun ci amanarsa.

Nasir El-Rufa'i ya yi zargin suna hada masa makarkashiya tare da neman kawo karshen tasirin siyasarsa a jihar Kaduna da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

2027: An gano manyan dalilai 2 da suka sanya El Rufai ya bar APC, ya koma SDP

A halin yanzu tsohon gwamnan ya fito ya fadawa duniya cewa Uba Sani ba abokinsa ba ne.

3. Jawo 'makiyan' El-Rufa'i zuwa APC

A shekarun baya, El-Rufai ya shiga takun saka da wasu ‘yan siyasa a Kaduna, ciki har da Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi.

Sai dai yanzu, wadannan mutanen da wasu ‘yan adawa da suka taba gwabza wa da shi sun koma APC, har ta kai Sanata Hunkuyi ya samu mukamin a gwamnati.

Haka kuma a wani taro da aka gudanar a Kaduna, Hunkuyi ya shawarci El-Rufa'i ya gaggauta neman yafiyar mutanen da ya zalunta a lokacin da ludayinsa ke kan dawo.

Makiyan Malam Nasir El-Rufai sun zama na kusa da gwamnatin Uba Sani yau a Kaduna.

4. Binciken jami'an gwamnatin El-Rufa'i

Bayan barinsa mulki, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta fara bincike kan wasu mutane da suka yi aiki a karkashinsa.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: Nasir El Rufai ya fitar da sanarwar ficewa daga APC zuwa SDP

Daga cikin mukarraban gwamnatin El-Rufa'i da ake zargi da almudahana akwai Jimmi Lawal da Muhammad Bashir Sa'idu, wadanda ke hannun hukuma a yanzu.

Wannan kwamitin ya binciki yadda gwamnatin El-Rufai ta tafiyar da kudi, musamman ma batun basukan da jihar ta ciyo.

Kwamishinonin da suka yi aiki da 'dan siyasar sun karyata zargin majalisa da ICPC.

5. El-Rufa'i: "Gwamnati ta yi biris da shawarwari"

El-Rufai na daga cikin manyan jiga-jigan da suka goyi bayan Bola Tinubu a zaben 2023, kuma ya na daga cikin masu ba da shawara kan harkokin mulki.

Sai dai bayan kafa gwamnati, ana ganin an kau da kai daga shawarwarinsa, musamman ta fuskar tafiyar da tsaro da tattalin arzikin kasa.

Bayan batun sulhu da 'yan bindiga, shigo da abinci daga ketare, El-Rufai ya soki yadda ya ce aka bar jahilai suna tafiyar da sha'anin jam'iyya.

Nasir El-Rufa'i ya fice daga APC

Kara karanta wannan

Nasir El Rufa'i ya sauya sheka, ya fita daga APC zuwa SDP

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sanar da ficewarsa daga APC a ranar Litinin, 10 ga Maris, 2025 bayan ya dade yana ja da gwamnati.

El-Rufai ya bayyana cewa ya ajiye shaidarsa ta zama dan jam'iyya, bayan ya tattauna da abokansa, magoya bayansa, da sauran masu ruwa da tsaki a cikin jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng