Gwamnan Kaduna Ya Yi Gargadi kan Siyasantar da Tsaro bayan Kalaman El Rufai

Gwamnan Kaduna Ya Yi Gargadi kan Siyasantar da Tsaro bayan Kalaman El Rufai

  • Gwamnatin Uba Sani ta bayyana rashin jin dadin yadda wasu 'yan siyasa ke kokarin siyasantar da lamarin tsaro a Kaduna
  • Gwamnan ya fadi haka ne a wani taron karbar mutane 58 da jami'an tsaro suka samu nasarar ceto wa daga wasu 'yan ta'adda
  • Ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan da suka dace game da masu yada labaran karya a kan tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya gargadi ‘yan siyasa da su guji siyasantar da batun tsaro, yana mai cewa irin wannan mataki yana jefa rayukan fararen hula cikin hadari.

Duk da cewa bai ambaci sunan wani dan siyasa ba, gargadin ya zo ne bayan da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya zargi Uba Sani da Nuhu Ribadu, da siyasantar da lamarin tsaro.

Kara karanta wannan

Ana neman Turji, wani ɗan bindiga da yaransa sun ba da mamaki, sun mika wuya

Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya yi wa 'yan siyasa kashedi Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamna Uba Sani ya yi wannan gargadi ne a lokacin da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Kaduna, a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan taro ne gwamnan ya tarbi mutane 58 da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga a jihar ta Kaduna da zummar mika su ga 'yan uwansu.

Gwamnan Kaduna ya soki wasu ‘yan siyasa

A cewar jaridar Daily Trust, gwamna Uba Sani ya yi Allah-wadai da masu amfani da rashin tsaro domin cimma muradun siyasa, tare da daukar alkawarin daukar mataki a kansu.

Ya ce:

“Masu cin moriyar rashin tsaro ba za su ji dadin ceto wadannan bayin Allah ba, domin su suna amfana da rashin zaman lafiya."

“Gwamnatin Kaduna a tsaye take,” Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya jaddada kudirin gwamnatinsa na dawo da zaman lafiya a jihar, yana mai nuni da nasarorin da aka samu ta hanyar shirin dawo da zaman lafiya na jihar.

Kara karanta wannan

Fitinannen dan ta'addan da ya addabi Zamfara, Nabamamu ya fada tarkon sojoji

Kaduna
Gwamnatin Kaduna ta ce za ta tabbatar da zaman lafiya a jihar Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Ya ce shirin da gwamnatinsa ta bijiro da shi ya taimaka wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ke fama da rikici kamar Birnin Gwari.

Ya ce:

“Ta hanyar tsarin zaman lafiya na Kaduna, wanda ke amfani da dabarun zaman lafiya maimakon amfani da karfi, Birnin Gwari da aka dauka a matsayin yankin da ba a iya shiga, yanzu an samu kwanciyar hankali.

Uba ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga kamar Kauru, Kajuru da Kachia.

Gwamnan Kaduna ya yi kashedi ga ‘yan siyasa

Gwamnan ya yi gargadi cewa ko da yake yana maraba da adawar siyasa, ba zai yarda da masu amfani da rashin tsaro domin cimma burinsu ba.

Uba Sani ya kuma soki masu yada bayanan da ba su da tushe a kafafen sada zumunta domin bata sunan gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ce:

“Siyasantar da tsaro ba adawa ba ce. Wadanda ke yada karya a kafafen sada zumunta ba su damu da talakawa ba; suna kawai neman cimma bukatunsu na kashin kai."

Kara karanta wannan

Dakaru sun yi dirar mikiya a kan 'yan ta'adda ana tsaka da karbar kudin fansa

Kaduna: An ceto wadanda aka yi garkuwa da su

Gwamna Sani ya bayyana cewa wadanda aka ceto sun samu kulawar kwararru na tsawon kwanaki 11, aka yi jinyarsu tare da duba lafiyar kwakwalwa.

Ya ce an dauki nauyin kula da su ne da taimakon gwamnatin jihar Kaduna, kuma har yanzu akwai mutum daya da ke ci gaba da karbar magani.

Haka kuma, ya yi alkawarin tallafa wa wadanda aka ceto da kudi domin farfado da rayuwarsu, ciki har da bayar da tallafin kasuwanci da noma.

"Tsaya a matsayinka," Kwamishinan Kaduna ga El-Rufa'i

A baya, kun ji cewa Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarauta na Kaduna, Alhaji Sadiq Mamman Lagos ya zargi Nasir El-Rufa'i da ya wa gwamnatinsu katsalandan.

Ya ce wannan ba daidai ba ne, ya kuma bukaci tsohon gwamnan da ya rike girmansa tare da gujewa kalamai marasa dadi kan gwamnatinsu da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.