'Jihar Gurara': Bayani kan Sabuwar Jiha da Ake So a Kirkira a Kudancin Kaduna
- Wata kungiyar Kudancin Kaduna ta ƙara zage damtse wajen ganin majalisar tarayya ta ƙirƙiri jihar Gurara, mai kananan hukumomi 12
- Kungiyar ta kafa kwamitin da Barista Mark Jacob ke jagoranta don tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da cika ƙa’idodin kirkirar jihar
- Masu fafutukar sun ce Gurara tana da girman kasa, albarkatun noma da ma’adinai, wanda zai sa ta dogara da kanta idan aka kirkire ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Kungiyar mazauna Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta sake daura damara da zage damtse na ganin majalisar tarayya ta kirkiri jihar Gurara.
An ce mambobin kungiyar sun sake daukar salon tuntuba da mika kokon bararsu a duk inda suka san za su samu biyan bukata don kirkirar sabuwar jihar.

Asali: Twitter
Ana so majalisa ta kirkiri jihar Gurara

Kara karanta wannan
Ana fama da tsadar rayuwa, gwamna a Arewa zai fara tatsar haraji daga masu gidaje
Kungiyar SOKAPU, ta samu kwarin gwiwar yin hakan bayan majalisar wakilai ta sake ba da damar gabatar da bukatun kirkirar sababbin jihohi, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabuwar damar da kwamitin gyaran kundin tsarin mulki ya bayar ta sa kungiyar SOKAPU ta fara inganta shirin ta don cika ƙa’idodin kirkirar jihar Gurara a dokance.
A wannan gabar ne ƙungiyar ta kafa kwamitin da Barista Mark Jacob ke jagoranta don tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a matakin jiha da ƙasa.
SOKAPU ta samu goyon baya gwamnan Kaduna
Shugaban SOKAPU, Solomon Tabara, ya bayyana cewa kwamitin ya samu goyon baya daga ‘yan majalisa da wasu fitattun mutane da masu fada a ji.
Solomon ya kuma musanta jita-jitar cewa Gwamna Uba Sani ba ya goyon bayan ƙirƙirar jihar Gurara, yana mai nuna hujjoji na goyon bayansa.
“Maganar cewa gwamnan ba ya goyon bayan kirkirar jihar Gurara ba gaskiya ba ce. Hujjoji na nuna akasin haka,” inji Solomon .

Kara karanta wannan
Bayan ƙarewar wa'adin sa'o'i 48, gwamna na neman tattago rigima da Majalisar Dokoki
Ya buƙaci al’ummar Kudancin Kaduna da su kasance masu haɗin kai tare da gujewa duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Kungiya ta fadi tasirin kirkirar jihar Gurara

Asali: Twitter
Shugaban na SOKAPU ya bayyana cewa jihar Gurara da ake so a kirkira ta ƙunshi kananan hukumomi 12, kuma tana da girman da ya zarce wasu jihohi.
Ya ce jihar Gurara, tana da albarkatun noma da ma’adinai masu yawa, wanda ke nuna cewa za ta iya dogara da kanta idan an ƙirƙire ta.
Solomon ya ce yanzu da majalisar wakilai ta bude kofar karbar bukatun kirkirar jihohin, SOKAPU na aiki tukuru don ganin an cika duk sharuddan doka.
Yayin da aikin gyaran kundin tsarin mulki ke gudana, ƙungiyar na fatan burin da ta dade tana ci, a wannan karon zai zama gaskiya.
An gabatar da bukatar kirkirar jihohi 35
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin majalisar wakilai kan gyaran kundin tsarin mulki ya ce an karɓi bukatun ƙirƙirar sabbin jihohi 31 daga sassan Najeriya shida.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun yi bayanin yadda bindigogi kusan 4,000 suka bace a karkashin kulawarta
Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ya karanta wasika da ta bayyana sharuddan da dole ne a bi kafin a amince da ƙirƙirar sababbin jihohi.
Wasikar ta nuna cewa sashe na takwas na kundin tsarin mulki ya tanadi amincewar kashi uku na ‘yan majalisa kafin a kafa wata jiha.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng