El Rufa'i: Kotu Ta Umarci ICPC Ta Kwato sama da N1bn da Aka Karkatar a Kaduna
- Babbar kotun tarayya ta zartar da hukunci kan bukatar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gabatar a kan tsohuwar gwamnatin Kaduna
- ICPC ta shaida wa kotu cewa ta gano sama da N1bn da tsofaffin jami’an gwamnatin Kaduna su ka karkatar, maimakon aiwatar da aikin titin jirgin kasa
- Mai shari’a H. Buhari ya amince da rokon lauyan ICPC, ya kuma ba da umarni a yi shela domin duk mai kalubalantar hukuncin ya gabatar da hujjarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta bayar da umarnin kwato N1.37 biliyan da ake zargin an karkatar daga baitul malin Gwamnatin Jihar Kaduna zuwa wani asusun sirri.
Wannan kudi, wani bangare ne na abin da aka fitar domin aikin jirgin kasa na zamani da ba a kai ga aiwatar wa ba a zamanin mulkin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.

Asali: Facebook
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa mai shari’a H. Buhari ne ya ba da umarnin kwace kudin na wucin gadi a ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan da ICPC ta shigar da bukatar a gaban kotu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ICPC ta bayyana cewa ta gano kudin a cikin wani asusun sirri, wanda ya saba wa dokar yaki da cin hanci da rashawa.
ICPC ta nemi kwato kadarorin gwamnatin Kaduna
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, a ranar 14 ga watan Fabrairu ne hukumar yaki da cin hanci ta shigar da bukatar kwato wadannan kudi a gaban kotu.
ICPC ta ce gwamnatin El-Rufai ba ta aiwatar da aikin da aka fitar da kudin ba, wanda hakan ya hana al’ummar Kaduna cin gajiyar tsarin sufuri na jirgin kasa da aka shirya yi da dukiyar.
Hukumar ta ce wasu jami’an gwamnatin Kaduna ne suka karkatar da kudin ta hanyar kamfanin Indo Kaduna MRTS JV Nig. Ltd.
Kaduna: Kotu ta amince da bukatun ICPC
Lauyan ICPC, E.O Akponimisingha, ne ya gabatar da bukatar hukumar a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Rahotannin sun nuna tun da zaman shari’ar na musamman ne, ba a ba wa wadanda ake tuhuma damar kare kansu a kotu ba.
Bayan amincewa da bukatar kwace kudin na wucin gadi, alkalin kotun ya umurci hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta wallafa sanarwa a cikin jaridu biyu na kasa a kan batun.

Asali: Twitter
An bukaci ICPC ta wallafa bukatar duk wani da ke da takaddama a kan kudin, ya gabatar da bukatarsa a kotu, inda zai nuna dalilin da zai hana a kwace kudaden don mayar da su ga gwamnati.
Alkalin kotun ya daga sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu domin ba wa duk wanda ke da bukatar neman kudaden damar gabatar da hujjarsa a gaban kotu.
ICPC ta zargi gwamnatin El Rufa'i da rashawa
A baya, kun samu labarin cewa Hukumar taki da Rashawa ta ICPC ta gurfanar da wasu mukarraban tsohon gwamnan Kaduna, Nasiru El-Rufai a gaban kotu bisa zargin almundahana.
Tsofaffin mukarraban sun hada da Lawal Adebisi, tsohon mai bai wa gwamna shawara, Umar Waziri, tsohon Akanta Janar, da Yusuf Inuwa, tsohon kwamishinan kudi kan zargin wawashe N64m.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng