Tsohon Sanatan Kaduna Ya Yi Magana da El Rufai Ya Sauya Sheka daga APC zuwa SDP

Tsohon Sanatan Kaduna Ya Yi Magana da El Rufai Ya Sauya Sheka daga APC zuwa SDP

  • Sanata Shehu Sani ya yi shaguɓe da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa SDP
  • Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya ya tuna yadda aka kore su daga APC a kakar zaɓen 2019, yana mai cewa a yanzu Allah ya masu sakayya
  • Wannan kalamai na Shehu Sani na zuwa ne bayan El-Rufai ya tabbatar da cewa ya bar jam'iyyar APC da yana cikin waɗanda suka kafa ta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya kuma mai rajin kare hakkin bil'adama, Shehu Sani, ya yi magana kan sauya shekar Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP.

Shehu Sani ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna ya kore su daga gidansu zuwa jeji, yanzu kuma Allah ya masu sakayya.

Sanata Shehu Sani.
Sanata Shehu Sani ya yi wa El-Rufai shaguɓe da ya sauya sheka zuwa SDP Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Sanata Shehu Sani ya yi wannan furucin ne a wani gajeren saƙo mao cike da sarƙaƙiya da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Litinin, 10 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka jawo El Rufai ya yi sallama da APC, ya burma jam'iyyar SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehu Sani ya yiwa El-Rufai shaguɓe

Tsohon Sanatan ya nuna cewa abin da ya faru da El-Rufai tamkar hukuncin Ubangiji ne bisa abubuwan da suka gabata.

Ya ce:

"Ya kore mu daga gidajenmu ya tura mu cikin daji, sai Ubangiji ya kore shi daga gidansa ya tura shi cikin jeji. Wannan shi ne hukuncin Ubangiji."

Duk da cewa bai ambaci sunan El-Rufai kai tsaye ba, ana ganin wannan magana na da nasaba da rikicin da suka sha yi tun lokacin da El-Rufai ke gwamna.

Tarihin rashin jituwar Shehu Sani da El-Rufai

Shehu Sani da El-Rufai sun daɗe suna gaba da juna tun lokacin da tsohon gwamnan ke mulkin Kaduna daga 2015 zuwa 2023.

A lokacin gwamnatinsa, El-Rufai ya gudanar da rusau a wurare da dama a Kaduna, ciki har da gidajen da suka yi shekaru da dama ana zama.

A wancan lokacin, Shehu Sani ya kasance ɗaya daga cikin masu sukar matakin na El-Rufai, yana zargin gwamnan da yin hakan don cin zarafin wasu mutane.

Kara karanta wannan

2027: An gano manyan dalilai 2 da suka sanya El Rufai ya bar APC, ya koma SDP

Haka nan kuma El-Rufai ne ya jagoranci karya Shehu Sani har ya rasa damar sake komawa Majalisar Dattawa a zaɓen 2019.

El Rufai da Shehu Sani.
Shehu Sani ya saki sako bayan sauya shekar El-Rufai Hoto: Nasir El-Rufai, Shehu Sani
Asali: Facebook

"Allah ne Ya saka mana" - Shehu Sani

Yanzu da gidan siyasar tsohon gwamnan ya rushe a APC, Shehu Sani ya yi amfani da wannan damar don bayyana cewa lamarin tamkar hukuncin Allah ne a kan El-Rufai.

Ana ganin dai kalaman Shehu Sani na nufin cewa Allah ya kore Nasir El-Rufai daga APC kamar yadda shi ma ya kore su a shekarun baya.

Dalilin da suka kori El-Rufai daga APC

A wani rahoton, kun ji cewa an gano dalilin da ake kyautata zaton su ne suka tilastawa Nasir El-Rufai ya tattara kayansa ya bar jam'iyyar APC zuwa SDP.

Mallam Nasir El-Rufai yana daya daga cikin wadanda suka assasa kafuwar jam'iyyar APC a Najeriya, kuma ya taka rawa har ta ci zaben farko a 2015.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262