Seyi Tinubu da Minista Sun Dira Gidan Buhari a Kaduna, An Yada Bidiyon
- Ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, da Ministan Matasa, Ayodele Olawande, sun kai ziyara ta musamman gidan tsohon shugaban ƙasa
- Malam Bashir Ahmad, tsohon hadimin Buhari, ya tabbatar da ziyarar a daren Talata, 4 ga watan Maris, 2025, ta shafinsa na X
- Babu cikakken bayani kan abin da suka tattauna, amma ana ganin ziyarar da ta girmamawa yayin da ake buda bakin Ramadan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Ɗan shugaban kasa, Bola Tinubu ya kai ziyara ta musamman gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jihar Kaduna a yau Talata.
Seyi Tinubu tare da ministan harkokin matasa, Ayodele Olawande da wasu abokansa sun kai ziyarar gidan Buhari da ke jihar Kaduna.

Asali: Facebook
Seyi Tinubu ya tara yan APC, NNPP
Tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad shi ya tabbatar da haka a daren yau Talata 4 ga watan Maris, 2025 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dunkule siyasar Kano da ya tara ƙusoshin jam'iyyar APC mai mulki da NNPP suka yi buɗa baki.
Ɗan shugaban ƙasar ya yi buɗa baki da jiga-jigan ƴan siyasar ne ranar Litinin 3 ga watan Maris din 2025 a masallacin Al-Furqan da ke kwaryar birnin Kano.
Kafin wannan liyafar buɗa baki, ɗan shugaban kasar ya ziyarci fitaccen ɗan kasuwar nan, Aminu Ɗantata a gidansa da ke jihar.

Asali: Facebook
Kaduna: Bidiyon Seyi Tinubu a gidan Buhari
Tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad a cikin rubutunsa ya ce:
"Seyi Tinubu tare da Ministan Raya Matasa, Ayodele Olawande da abokansa sun ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna yau Talata."
Martanin wasu yan Najeriya game da ziyarar:
Yan Najeriya da dama sun yi martani bayan ziyarar Seyi Tinubu zuwa gidan Buhari inda da yawa suka caccaki salon mulkin tsohon shugaban kasar.
Neat_Ustaz:
"Abin a yaba ne."
Hubert crypt Blaine:
"Shugaban kasar da ba a taba yin irinsa ba wurin lalacewa."
Abiola Jamiu:
"Allah zai yi maganinsu gaba daya"
BIG GOD:
"Kuma talauci na ci gaba da bunkasa a Najeriya."
Kingxlye:
"Mafi munin shugaban kasa da aka taba yi a tarihin Najeriya kenan."
Dan Mai Karfi:
"Buhari mugun dan duniya ne, mene kuma 'ina tunanin lafiya ta kalau'"
Muwafaq:
"Sun kyauta."
AMBASSADOR JOE:
"Abin kunya ne, dukansu batattu ne."
CaptainNigeria:
"Waye ne kuma Seyi Tinubu?"
cryptomnia:
"Assalamu alaikum, malam Bashir a ina Baba ake tafsir?"
Buhari ya koma jihar Kaduna da zama
Kun ji cewa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya koma jihar Kaduna da zama karon farko tun bayan barinsa mulkin a watan Mayun 2023.
Buhari ya koma Kaduna bayan shafe shekaru biyu a garin Daura inda yake zaune tun a karshen watan Mayun 2023 bayan hawan Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan
Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu ya yamutsa siyasar Kano a wurin buɗa bakin azumi
Ya samu rakiyar mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da gwamnoni kamar Babagana Zulum na Borno da Uba Sani na Kaduna da tsofaddin ministoci da jiga-jigan gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng