Yaki da ta'addanci a Najeriya
Manoma sun shiga tsahin hankali a wasu ƙauyuka akalla 15 da ke jihar Taraba biyo bayan ayyukan 'yan bindiga wanda ya tilasta musu hakura da amfanin gonakinsu.
Ministan harkokin cikin gida na tarayya, Mista Tunji Ojo ya bayyana cewa matsalar tsaro ce ta sanya iyaye suka daina tura yaransu makarantu a faɗin ƙasar nan.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ƙaɗa kassara ƙungiyar 'yan ta'adda da ta hana al'umma zaman lafiya a dajin Sambisa na jihar Borno, an sheƙe su da dama.
Mai martaba Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya ce ba zai lamurci masu unguwanni su haɗa baki da vara gurbi ana hana jama'a zaman lafiya ba.
Wasu tsagerun 'yan bindigan daji sun harbe mutum uku har lahira a yankin ƙaramar hukumar Logo da ke jihar Benuwai, daga ciki har da 'yan sa'kai guda biyu.
Wasu tsagerun 'yan fashin daji sun sake kai hari wata majami'a a kudancin jihar Kaduna da daren ranar Alhamis, sun halaka matamin da ke koyon aiki, Ɗanlami.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma ministan tsaron Najeriya, Muhammad Vadaru Abubakar, ya buƙaci yan Najeriya su tallafa wa gwamnati da addu'a kan rashin tsaro.
Wasu tsagerun 'yan bindigan daji sun tashi mutanen ƙauyuka sama da 15 yayin da su ka kai wani kazamin hari jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sani Shinkafi, tsohon shugaban kwamitin hukunta masu aikata laifukan 'yan bindiga na jihar Zamfara ya yi kira ga NYSC ta daina tura matasa jihohin arewa 3.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari