Bauchi: Sarkin Ningi Ya Yi Barazanar Tsige Sarakunan Da Ke Taimakon Yan Bindiga

Bauchi: Sarkin Ningi Ya Yi Barazanar Tsige Sarakunan Da Ke Taimakon Yan Bindiga

  • Sarkin Ningi ya yi barazanar tsige duk hakimi ko mai Anguwan da ya kama da hannu a ayyukan bara gurbin yan bindiga
  • Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya ce rahoton da masarautarsa ta samu ya nuna akwai haɗin bakin wasu masu unguwanni a matsalar tsaro
  • Ya ce Masarautarsa ba zata lamurci haka ba, ya bai wa Sarakunan mako biyu su magance matsalar tsaro a yankunansu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Bauchi - Sarkin Ningi a jihar Bauchi a Arewa maso Gabas, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya gargaɗi dukkan masu riƙe da Sarauta a karakashin masarautarsa.

A rahoton Daily Trust, Sarkin ya yi barazanar tuge rawanin duk wani Hakimi ko mai Anguwan da ya gano yana da hannu a ayyukan 'yan bindigan daji a yankin da yake jagoranta.

Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammadu Danyaya, ya gana da Masu Unguwanni.
Bauchi: Sarkin Ningi Ya Yi Barazanar Tsige Sarakunan Da Ke Taimakon Yan Bindiga Hoto: Abdul'aziz Idris Salihu
Asali: Facebook

Fitaccen Basaraken ya yi wannan gargaɗin ne a wurin taron sarakunan gargajiya wanda ya ƙunshi Hakimai da masu Unguwanni na faɗin ƙasar Masarautar Ningi.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Taɓarya Har Ya Mutu Kan Ƙaramin Abu

Alhaji Ɗanyaya ya bayyana cewa wani rahoton sirri da Masarautarsa ta samu ya nuna akwai haɗin bakin wasu masu Unguwanni a ayyukan ɓata gari da ta'addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin ya kara da cewa rahoton tsaron ya kuma nuna cewa wasu masu unguwanni suna gayyatar 'yan uwansu da su zo masarautar Ningi don yin sana'ar garkuwa da mutane.

Wane mataki Sarkin ya fara ɗauka a yanzu?

Sarkin ya ce ba zai lamurci Sarakuna su haɗa baki da ɓata gari da bara gurbu wajen hana al'umma zaman lafiya ba, inda ya ce a shirya yake ya tuɓe rawanin ko waye.

A cewarsa, Masarautar zata gudanar da bincike maizrfi kan kowane Mai Unguwa na gunduma da nufin zaƙulo bara gurbin kwai daga cikinsu.

Bugu da ƙari, Sarkin ya bai wa Hakimai da Dagattai wa'adin mako biyu su kawo ƙarshen kalubalen tsaron da ya addabi yankunan da ke ƙarƙashinsu.

Kara karanta wannan

Annoba Ta Aukawa Abuja, Mutane Rututu Sun Sheka Barzahu a Birnin Tarayya

Ya kuma ba su umarnin cewa da zaran sun ga motsin wasu miyagu da ba a gane ba, su gaggauta kai rahoto ga hukumomin tsaro domin ɗaukar mataki.

Da yake maida martani a madadin Sarakunan Gargajiya, Alh Ya’u Shehu Abubakar, Hakimin Burra, ya tabbatar wa sarkin cewa za su bi duk umarnin da ya ba su.

Tashin Hankali Yayin da Jirgin Sama Ya Gamu da Hatsari Bayan Ya Sauka a Legas

A wani rahoton na daban kuma Wani jirgin sama da ya taso daga Owerri, jihar Imo ya gamu da matsala yayin sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas.

Jirgin ya samu matsalar da ta kai ga sauka daga asalin titinsa na tashi ko sauka, lamarin da ya haifar da firgici da tashin hankali tsakanin Fasinjoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel