'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wurin Ibada, Sun Kashe Malami a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wurin Ibada, Sun Kashe Malami a Kaduna

  • 'Yan bindiga sun sake kai hari wata majami'a da ke Fadan Kamantan a yankin Kafanchan da ke kudancin jihar Kaduna
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun banka wuta a ɗaya daga cikin gidajen da ke ƙarƙashin Cocin, lamarin da ya yi ajalin mutum ɗaya
  • Har yanzu ba bu wani bayani daga gwamnati ko hukumar 'yan sanda amma shugaban CAN na jihar ya ce lamarin babban abin takaici ne

Jihar Kaduna - Wasu miyagun 'yan bindigan daji sun kai farmakin rashin imani kan Cocin St. Raphael Parish da ke garin Fadan Kamantan yankin Kafanchan a kudancin jihar Kaduna.

Jaridar Punch ta tattaro cewa yayin harin na daren Alhamis, 'yan bindigan sun ƙone ɗaya daga ciki gidajen Cocin tare da wani mai shirin zama Malamin Coci, Na’aman Danlami.

Harin yan bindiga a Kaduna.
'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Wurin Ibada, Sun Kashe Malami a Kaduna Hoto: punch
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa yayin da sauran Fastocin Cocin suka yi nasarar tsira da rayuwarsa, ibtila'in ya rutsa da Ɗanlami, ɗalibin da ke koyon fara wa'azi da zama Fasto.

Kara karanta wannan

Tinubu: Gwamnan PDP Ya Manna Hotonsa a Jikin Buhunan Shinkafa, Ya Faɗi Dalili

An ce tuni aka ɗauki gawarsa aka kai ɗakin ajiyar gawarwaki bayan ya mutu sanadiyar wutar da maharan suka banka a gidan Cocin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma shugaban ƙungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar ta wayar salula.

"Babban abin takaici ne yadda lamarin kashe-kashen rayuka da irin waɗan nan ayyukan sheɗancin ke ci gaba da faruwa," in ji Rabaran Hayab.

Yadda lamarin ya faru da daddare

Wani ganau ya shaida wa gidan Talabijin na Channels cewa ‘yan bindigan da yawansu ya kai yawa sun kai farmaki cocin Saint Raphael Parish da ke Fadan Kamatan da daddare.

Ya ce yayin harin, yan bindigan sun banka wa ginin wuta tare da motocin da ke ajiye a harabar ginin.

Kara karanta wannan

Bidiyoyi Da Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ganduje, Keyamo, Bala Mohammed Da Sauransu Ke Likimo a Kotun Zaben Shugaban Kasa

Majiyoyi sun bayyana cewa Maryagi Ɗanlami ya rasa rayuwarsa ne sakamakom hayaƙin da ya shaƙa sa'ilin da yake ƙoƙarin guduwa.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Jim kadan bayan faruwar lamarin, rundunar ‘yan sanda a jihar ta bayyana cewa tuni jami'anta suka kaddamar da farautar maharan.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Manir Hassan, ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki cibiyar ibadar da yawa.

Jami'an DSS Sun Kama Masu Karkatar da Tallafin Gwamnati a Jihar Nasarawa

A wani rahoton na daban Hukumar DSS ta kama ma'aikatan gwamnati bisa zargin wawure wasu kayan tallafin da FG ta samar domin raba wa yan Najeriya.

Mai magana da yawun DSS, Peter Afunanya, ya ce a halin yanzu anɓkama wasu a jihar Nasarawa kuma an kwato kayan da suka ɗiba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel