Yaki da ta'addanci a Najeriya
Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, an kama wasu tsagerun da ke addabar mutane a jihohin kasar nan, musamman ma Arewacin Najeriya a watanni kasa da tara.
Jami'an hukumar 'yan sanda sun kubutar da wani bawan Allah yayin musayar wuta mai ban tsoro da 'yan ta'adda da sanyin safiyar ranar Jumu'a a jihar Katsina.
Wasu 'yan bindiga sun farmaki motar sintirin rundunar sojin Najeriya a Benin City, babban birnin jihar Edo ranar Laraba da ta shuɗe, sun yi ajalin soja ɗaya.
Shugaban sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya shiga wata yarjejeniya ta ƙawance na soji, da kasashen Mali da Burkina Faso.
Ministan tsaron Burtaniya, James Heappey MP, ya ƙara kawo ziyara Najeriya kuma ya gana da Badaru, Bello Matawalle, da manyan hafsoshin tsaron ƙasa a Abuja.
Sabbin ministocin tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar da Bello Matawalle sun sha alwashin kawo sauyi mai kyau a fasalin tsaron ƙasar nan cikin shekara 1.
Kabiru Ahmadu, ɗan majalisar wakilan tarayya daga jihar Zamfara ya ce yan fashkn jeji sun zafafa kai hare-hare kan jama'a ba don komai ba don a tattauna da su.
Rundunar sojojin Najeriya sun kutsa mafakar ‘yan ta’adda a garin Dikwa. A sanadiyyar haka aka iya kubutar da Mary Nkeki wanda ta rabu da iyayenta a Chibok.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirin ɗaukar sabbin mambobin ƙungiyar 'yan bijilanti 7,000 domin dawo da zaman lafiya.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari